Nigerian news All categories All tags
Ina nan a cikin APC ba inda zanje – Sanata Marafa

Ina nan a cikin APC ba inda zanje – Sanata Marafa

- Ana ta rade-radin cewa 'yan jam'iyyar APC da yawansu zasu sauya sheka kafin zaben 2019

- Ciki har da sanatan jihar Zamfara Kabiru Marafa

- Amma sai dai yanzu ta fito fili cewa ba ya daga cikin wadancan da ake hasashen

Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa shi da sauran 'yan uwansa yan majalisu wadanda aka zabe su karkashin tutar Jamiyyar APC ba su da sha'awar fita daga Jamiyyar ta APC.

Ina nan a cikin APC ba inda zanje – Sanata Marafa

Ina nan a cikin APC ba inda zanje – Sanata Marafa

Tun da farko dai kafafen yada labarai sun sha rawaito cewa Kabiru Marafan yana daga cikin wadanda za su fice daga Jamiyyar ta APC, wanda shi kuma ya musanta hakan.

KU KARANTA: Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da bada hadin kai wajen yaƙar cin hanci da rashawa

"Bani da masaniya akan wannan maganar ta ficewa daga Jamiyyar APC kuma ban san daga ina ta samo tushe ba. Ban taba tataunawa da wani ba, kuma haka zalika ban taba halartar taron da yan sabuwar R-APC su ke yi ba" in ji sanatan.

A karshe ya bayyana irin gudummawar da ya ke baiwa Jamiyyar ta APC, wacce yana daga cikin wadanda su ka kafa ta. Ya kuma ce babu shakka Jamiyyar zata kawo karshen dukkanin wasu matsaloli ba ma na cikin gida kadai ba, har da matsalolin da su ka addabi kasar nan ba ki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel