Nigerian news All categories All tags
Rundunar sojin Najeriya sun yi arangama da yan Boko Haram a Mallam Matsari

Rundunar sojin Najeriya sun yi arangama da yan Boko Haram a Mallam Matsari

Jami’an sojin rundunar Operation Lafiya Dole da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya tare da jami’an Civillian JTF da aka fi sani da kato da sanda sun yi arangama da wasu yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram a kauyen Mallam Matsari da ke jihar Borno.

Kakakin hukumar sojin Najeriya, Birgediyar Janar Texas Chukwu, ya bayyana hakan ne ta shafin ra’ayi da sada zumuntar hukumar inda yace:

“Jami’an sojin operation LAFIYA DOLE tare da CJTF sun aiwatar da shara a Mallam Matsari inda sukayi akayi arangama da yan Boko Haram.

Amma yan ta’addan sun arce cikin kauyen yayinda suka hango jami’an tsaro kuma suka bar karamar yarinya.

Makaman da aka kwato sune : bindigar AK 47 guda 3, wayoyin hada bama-bamai, batura, da sauran su.”

Rundunar sojin Najeriya sun yi arangama da yan Boko Haram a Mallam Matsari

Rundunar sojin Najeriya sun yi arangama da yan Boko Haram a Mallam Matsari

Kakakin rundunar sojin Najeriya watau Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, shi ne ya shaidawa manema labarai cewa, kamar yadda ake gani rundunar ta su ta yi kokari wajen kakkabe 'yan Boko Haram, abin da ya rage yanzu saura yan kadan.

Legit.ng ta samu kuma dai Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ka kara da cewa sun bullo da wasu sabbin dabaru sun kuma samu muhimman kayan aiki domin idasa samun nasara a yakin da rundunar sojin ta ke da 'yan Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya sun yi arangama da yan Boko Haram a Mallam Matsari

Rundunar sojin Najeriya sun yi arangama da yan Boko Haram a Mallam Matsari

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel