Nigerian news All categories All tags
Da kudin damfara nake ciyar da mata 2 da yara 7 – Mai laifi

Da kudin damfara nake ciyar da mata 2 da yara 7 – Mai laifi

Jami’an yan sandan jihar Sokoto sun kama wani dan damfara, Mahmud Hamza, wanda ya shahara wajen karban kudade daga mutane da katin shaidar yan sanda.

Da ake gurfanar da mai laifin tare da wasu yan iska a hedkwatan rundunar dake jihar a ranar Juma’a, jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Cordelia Nwawe, ya bayyana cewa kwamishinan yan sandan jihar ya kaddamar da yaki da yan iska da sauran masu laifi a jihar.

Kakakin yan sandan ya shawarci iyaye da su ja kunnen ýaýansu wajen bin doka kamar yadda baza su dauki ayyukan laifi da wasa ba a jihar.

Da kudin damfara nake ciyar da mata 2 da yara 7 – Mai laifi

Da kudin damfara nake ciyar da mata 2 da yara 7 – Mai laifi

A wata hira da akayi da shi, Hamza yayi bayanin cewa ya samu katin shaidar ne daga wani dan sanda da ya mutu sannan ya manna hotonsa a jikin katin.

“Ni dan damfara ne sannan kuma na san cewa na aikata laifi amma ina neman afuwa, b azan sake aikata laifin ba idan aka kyale ni. Ni ba dan fashi bane, amma ni dan damfara ne, ina da mata biyu da yara bakwai sannan kuma du kina ciyar dasu daga kudin da na samu ta hanyar damfarar ne,” yayi bayani.

KU KARANTA KUMA: Son kyautatawa mata ta ne ya kai ni ga sata – Mai laifi

Yan sandan sun kuma kama wani Usman Danmaliki, wanda ke yin hayar jami’am yan sanda da aka kora suna karban kudade daga kauyawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel