Nigerian news All categories All tags
Fadar shugaban kasa tayi gargadi akan yada labaran karya

Fadar shugaban kasa tayi gargadi akan yada labaran karya

Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan Najeriya dama wadanda suke kasashen ketare dasu guji yada labaran kanzon kurege da kuma labaran bacin suna dangane da rikicin makiyaya da manoma

Fadar shugaban kasa tayi gargadi akan yada labaran karya

Fadar shugaban kasa tayi gargadi akan yada labaran karya

Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan Najeriya dama wadanda suke kasashen ketare dasu guji yada labaran kanzon kurege da kuma labaran bacin suna dangane da rikicin makiyaya da manoma.

Malam Garba Shehu, babban mai bawa shugaban kasa shawara a bangaren yada labarai, shine yayi wannan jan kunnen jiya a Abuja.

DUBA WANNAN: Wata mata mai ciki ta sha da kyar daga hannun masu satar mutane

Kamar yanda yace Gwamnatin tarayya tana aiki tare da Gwamnatin jihohi d da kuma hukumomin tsaro, tare da abokan huldar ta na kasashen ketare don ganin an kawo karshen matsalar.

Yace "rikicin makiyaya da manoman ya zama tarihi a yanzu."

"Chanjin yanayi, balle bushewar kogin Chadi, ya kara kawo matsi ga dayawan mutanen arewacin Najeriya, wanda hakan shine musabbabin abinda ya kawo matsalar.

"Kamar yanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada, akwai sa hannun wasu yan siyasa inda suke yin amfani da yan ta'adda don assasa kashe kashe a wasu wurare a kasar nan.

"Chanjin yanayi matsala ce da ta dami duniya kuma Gwamnatin Najeriya zatayi aiki da makwaftan ta don ganin ta kawo karshen matsalar. "

Yace Gwamnatin tarayya bata nuna banbanci ga kowa kuma tana aiki tukuru don ganin ta kare dukkan mutanen Najeriya.

"Da hadin kai ne muke da karfi a matsayin mu na kasa daya kuma da hadin kai ne zamu iya shawo kan kalubalen da ke damun mu," yace.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel