Nigerian news All categories All tags
Anyi garkuwa da wasu Mawaka a wata jiha a kasar nan

Anyi garkuwa da wasu Mawaka a wata jiha a kasar nan

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu fitattun mawaka guda 2 a Owerri, babban birnin jihar Imo

Anyi garkuwa da wasu Mawaka a wata jiha a kasar nan

Anyi garkuwa da wasu Mawaka a wata jiha a kasar nan

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu fitattun mawaka guda 2 a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Bacewar Ugo Stevenson da Izunna Obiakor, ya sanya mazauna garin cikin firgici da tashin hankali.

DUBA WANNAN: An kama mutane 11 da hannu a kashe - kashen jihar Zamfara

Majiyar mu tace an sace Stevenson a kusa da wani Banki, a hanyar shi ta zuwa gida. Obiakor kuma an sace shi ne lokacin da yake tuka motar shi mai kirar Jeep.

Stevenson, sanannen mawaki ne, marubuci sannan kuma mai nishadantarwa, ya samu kyaututtuka da dama na wakokin Najeriya, shi kuma Obiakor shine babban jami'in Twinstar Lightening and Stage House a Owerri.

Matar Stevenson ce ta tabbatar da sace shi, tace masu garkuwa da mutanen sun kirata tare da bukatar Naira miliyan 5 domin su sake shi.

Tace ta samu damar magana da mijinta. Ta kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun kira ta ne bayan da mijin ta yayi kwana biyu ba a san inda yake ba.

Tace "masu garkuwa da mutanen sun kira ni, suna bukatar Naira miliyan 5. An kuma bar mijina yayi magana dani."

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Andrew Enwerem, ya tabbatar da sace Stevenson, yace ana nan ana kokarin ceto shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel