Nigerian news All categories All tags
Rudani yayinda yan sanda suka karyata mutuwar Adikwu, tsohon jami’i da aka kama a fashin Offa

Rudani yayinda yan sanda suka karyata mutuwar Adikwu, tsohon jami’i da aka kama a fashin Offa

Rashin sanin inda Micheal Adikwu, dakataccen jami’in dan sanda da aka kama bayan ya jagoranci fashin bankin Offa a jihar Kwara da kashe jami’an yan sanda tara a harin, ya haifar da rudani saboda yan sanda sun daina gurfanar da shi.

An daina ganin Adikwu tun daga ranar Lahadi, 3 ga wan Yuni, a cikin yan fashin da ake gurfanarwa a taron manema labarai a hedkwatar rundunar, Abuja, sannan kuma tun daga lokacin ya daina bayyana a gaban jama’a.

Akwai rudani kan inda Adikwu yace kamar yadda wasu majiyoyi suka yi ikirarin cewa dakataccen dan sandan ya mutu a tsare.

Wata majiya ta ce: “Maganar gaskiya ita ce Micheal Adikwu ya mutu a tsare, don haka baza’a kara gurfanar da ba. Ya mutu a gaban sauran masu laifion, inda aka dauke gawarsa.”

Rudani yayinda yan sanda suka karyata mutuwar Adikwu, tsohon jami’i da aka kama a fashin Offa

Rudani yayinda yan sanda suka karyata mutuwar Adikwu, tsohon jami’i da aka kama a fashin Offa

Kafin mutuwar an rahoto cewa Adikwu ya fadi ngaskiyar cewa ya kashe jami’an yan sanda da dama da gan-gan a lokacin harin bankin Offa.

An rahoto cewa jami’in yayi ikirarin cewaya kashe jami’an yan sanda domin rama koransa daga rundunar da akayi wanda ya bayyana a matsayin rashinb adalci.

KU KARANTA KUMA: Son kyautatawa mata ta ne ya kai ni ga sata – Mai laifi

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanni ya karyata cewar Adikwu ya mutu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel