An kama mutane 11 da hannu a kashe - kashen jihar Zamfara

An kama mutane 11 da hannu a kashe - kashen jihar Zamfara

Yan sandan jihar Zamfara sun kara damke wasu mutane 11 da ake zargin da hannun su a kisan mutane 41 da akayi a karamar hukumar Zurmi a satin da ya gabata

An kama mutane 11 da hannu a kashe - kashen jihar Zamfara

An kama mutane 11 da hannu a kashe - kashen jihar Zamfara

Yan sandan jihar Zamfara sun kara damke wasu mutane 11 da ake zargin da hannun su a kisan mutane 41 da akayi a karamar hukumar Zurmi a satin da ya gabata.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan, SP Muhammad Shehu, yace hukumar ta kama mutane 11 na kungiyar 'Yansakai' a wuraren buyar su dake kauyen Kasuwan Daji dake karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: 2019: Kabilar Igbo sunce baza su zabi Atiku ba

Yace anyi kamen ne a safiyar ranar Asabar kuma sun samu nasarar kwace makamai masu yawan gaske, wadanda suka hada da bindiga wacce ke dauke da harsashi 68, wukake 8, adduna 3, layoyi da dai sauran su.

Kafin nan dai, kwamishinan yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya kai samame inda ya kama mutane 4 da ake zargin suma da hannun su a kashe kashen, inda ya tabbatar da cewa za a mika su ga kotu nan bada dadewa ba.

A cigaba da kawo karshen ta'addanci a yankin, hukumar ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin su da aikata ta'addanci a kauyen Bargaja dake karamar hukumar Gusau.

Mashin guda daya aka kama tare da su kuma za a mika su ga kotu in an kammala bincike, inji Shehu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel