Nigerian news All categories All tags
R-APC: Jam’iyyar adawa ta PDP ta kira wani taron gaggawa a Abuja

R-APC: Jam’iyyar adawa ta PDP ta kira wani taron gaggawa a Abuja

Mun samu labari cewa Jam’iyyar PDP ta kira manyan shugabannin ta domin ta zauna game da ‘Yan bangaren R-APC da ba mamaki su ke shirin dawowa cikin Jam’iyyar adawar a halin yanzu.

Jam’iyyar ta shirya zama yau dinnan ne game da yunkurin da wasu tsofaffi ‘Ya ‘yan ta ke yi na sauya sheka daga APC su dawo cikin ta. The Nation ta rahoto cewa PDP ta kira wani taro na musamman inda ‘Yan takarar ta za su halarta.

Yanzu haka Jam’iyyar ta PDP ta kira Atiku Abubakar, Makarfi, Lamido, Ibrahim Shekarau, Tanimu Turaki da sauran masu neman takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa domin su yi wani zama na musamman da bai wuce batun ‘Yan R-APC.

KU KARANTA: A kan Buhari na sha dauri sau 38 - Galadima

Ba mamaki manyan na PDP za su tattauna ne su gani ko za su karbi ‘Yan R-APC da ke shirin ballewa daga Jam’iyyar APC mai mulki. ‘Yan R-APC sun hada da Bukola Saraki, Yakubu Dogaram da irin su Rabiu Musa Kwankwaso.

Ba shakka PDP tuni ta sa wani kwamiti karkashin tsohon Gwamna Liyel Imoki ta zauna da ‘Yan R-APC. Shugaban Jam’iyyar dai ya aikawa masu neman takara da duk Gwamnoni da tsofaffin Ministocin PDP goron gayyatan taron na yau.

Prince Uche Secondus ya kuma ce Manyan Jam’iyyar na BOT da kuma Shugabannin Jam’iyyar na Jihohin kasar su na cikin wannan zama da za ayi a dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua a Auja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel