Nigerian news All categories All tags
Jirgin saman Najeriya zai fara zirga-zirga a Disamba - In ji Hadi Sirika

Jirgin saman Najeriya zai fara zirga-zirga a Disamba - In ji Hadi Sirika

- Ma'aikatar kula da harakokin sufurin jiragen sama ta kasa ta ce zuwa karshen shekara jirgin saman kasar zai fara aiki

- An dade dai ana burin ganin an dawo da jiragen sufurin sama na kasa mallakar gwamnatin tarayya

- Da alama wannan buri ya kusa cika idan har komai ya tafi dai-dai yadda aka tsara

Ministan ma'aikatar Hadi Sirika ya ce zuwa watan Disamban bana yake fatan kamfanin jiragen saman na kasar nan zai fara aiki.

Sai dai batun farfado da kamfani jirgin saman na hadin guiwa ne da 'yan kasuwa, inda ministan ya ce ita ce hanyar kawai da ta fi dacewa da za a dauki lokaci ana cin moriyarsa.

Jirgin saman Najeriya zai fara zirga-zirga a Disamba - In ji Hadi Sirika

Jirgin saman Najeriya zai fara zirga-zirga a Disamba - In ji Hadi Sirika

Ya jaddada hakan ne a yayin da yake karbar takardar shedar amincewa da yarjejeniyar kasuwanci daga babban jami'in hukumar kula da mika ragamar tafiyar da kadarorin gwamnati ga kamfanoni masu zaman kansu (ICRC), injiniya Chidi Izuwah.

Ya kuma ce gabatar da takardar shedar shi ne amincewa da matsayin da ake ciki ga aikin.

Ministan ya kuma musanta ikirarin da wasu ke yi cewa farfado da kamfanin jiragen saman na kasa zai durkusar da kamfanonin jiragen sama na 'yan kasuwa ke aiki a kasar.

KU KARANTA: Yanzu- yanzu: Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya shiga ganawar sirri da wasu gwamnonin APC

"Najeriya mai yawan jama'a sama da miliyan 180 tana da isassun hanyoyin da dukkanin jiragen da suka shirya wa kasuwanci za su iya aiki" in ji Sirika.

Jama'ar kasar nan mai karfin tattalin arziki a Afirka na dogaro ne da kamfanonin jiragen 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Jirgin saman Najeriya zai fara zirga-zirga a Disamba - In ji Hadi Sirika

Jirgin saman Najeriya zai fara zirga-zirga a Disamba - In ji Hadi Sirika

Wasu na ganin farfado da kamfanin jirgin saman zai taimaka wajen samun saukin tsadar farashin tikitin shiga jiragen sama na 'yan kasuwa da ake fama da shi.

Ko da yake kamfanonin jiragen saman na cewa dole kujerar jirginsu ta yi tsada saboda yawan kudaden harajin da suke biyan gwamnati.

Za a iya samun wadatuwar jiragen saman zuwa wasu sassa na kasar da jiragen 'yan kasuwa ba su zuwa idan kamfanin ya fara aiki.

A can baya kasar nan tana da kamfanin Air Nigeria da ke zirga-zirga a kasar har zuwa kasashen waje, amma kamfanin ya durkushe saboda wasu dalilai da ke da nasaba da sakaci daga bangaren gwamnati wajen kula da lafiyar jiragen da kuma sakaci da aiki daga ma'aikata.

Wanda kuma durkushewar kamfanin ya haifar da rasa ayyukan yi ga ma'aikata da dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel