Nigerian news All categories All tags
IGP ya umarci AIG da CP su sa ido domin ganin an zauna lafiya a Najeriya

IGP ya umarci AIG da CP su sa ido domin ganin an zauna lafiya a Najeriya

Mun ji labari cewa Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya watau IG Ibrahim Idris ya ja kunnen Kwamishinonin sa da sauran Mataimakan sa da su zura idanu kan masu tada rikici a sassan Kasar nan.

Ibrahim K. Idris ya nemi manyan Jami’an ‘Yan Sandan kasar su zama cikin shiri da kintsi a bakin aikin su. Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriyar ya bayyana wannan ne ta bakin Mai magana da yawun Rundunar kasar Jimoh Moshood.

IGP ya umarci AIG da CP su sa ido domin ganin an zauna lafiya a Najeriya

Shugaban 'Yan Sandan Najeriya IGP Idris K. Ibrahimya gargadi Jami'an sa

DCP Jimoh Moshood ya fitar da wannan jawabi ne kwanan nan bayan da wasu ‘Yan fashi da makami su ka kashe Jami’an ‘Yan Sanda har kusan 7 a Yankin Galadimawa da ke cikin babban Birnin Tarayya Abuja a wancan makon da ya wuce.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun gano cewa wata sabuwar ‘Darika ta bayyana a Najeriya

Shugaban ‘Yan Sandan kasar ya nemi Mataimakan sa watau AIG da ke Yankunan kasar da kuma Kwamishinonin Jihohi su ka zage dantse wajen sha’anin tsaron kasar. IG ya nemi CP da AIG su shirya Runduna da kayan aiki domin kare jama’a.

Shugaban ‘Yan Sandan na Najeriya ya kuma nemi Jami’an na sa su zura idanu a Masallatai da sauran wuraren bauta da kuma kasuwanni da makarantu da duk inda jama’a su ke zama domin ganin an yi maganin aukuwar wani tashin hankali.

‘Yan Sandan dai su na kokari ne wajen ganin cewa an yi maganin masu tada fitina a bangare da dama na cikin kasar nan. Kwanaki wani rikici da ya barke a Filato yayi sanadiyyar rashin dinbin mutane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel