Nigerian news All categories All tags
Dangote zai kashe Miliyan 500 wajen kafa cibiyar bincike a Jihar Katsina

Dangote zai kashe Miliyan 500 wajen kafa cibiyar bincike a Jihar Katsina

Mun samu labari tun a wancan makon da ya gabata cewa Aliko Dangote wanda shi ne Mai kudin kaf Nahiyar Afrika zai kashe wasu makudan kudi wajen kafa wani dakin bincike a Jihar Katsina.

Dangote zai kashe Miliyan 500 wajen kafa cibiyar bincike a Jihar Katsina

Dangote zai bude tsangayar binciken harkar noma a Katsina

Kamfanin Dangote za ta kashe kudi har Naira Miliyan 500 ne wajen kafa wata tsangayar binciken harkar noma a Jihar ta Katsina. Bayan nan kuma za a bude wajen sarrafa kayan amfanin gona duk a Garin na Katsina da ke Arewacin kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta buda wasu tituna a Arewa

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta bayyana cewa Aliko Dangote da Gwamnatin Jihar Katsina sun sa hannu kan wannan yarjejeniya da za ta bunkasa sha’anin noman zamani a Jihar a wancan makon.

Har wa yau labari ya zo mana cewa Jihar Katsina ta kuma dankawa kamfanin na ‘Dangote Kamfanin Katsina-Songhai na tsawon shekaru 10 kamar yadda mu ka ji. Wannan yarjejeniya za ta kare ne a shekarar 2028 kamar yadda ake sa rai.

Shi kuma Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya sallami wasu manyan Kwamshinoni da masu bada shawara a Gwamnatin sa kamar yadda mu ke samun labari yanzu. Ana dai kishin-kishin din cewa Gwamnan zai tattara ya bar APC kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel