Nigerian news All categories All tags
Mai uwa da wabe: Gwamnan APC da ake tunanin zai sauya sheka yayi zazzaga

Mai uwa da wabe: Gwamnan APC da ake tunanin zai sauya sheka yayi zazzaga

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya sallami wasu manya a Gwamnatin sa kamar yadda mu ke samun labari yanzu. Ana dai kishin-kishin din cewa Gwamnan zai tattara ya bar APC kwanan nan.

Mai uwa da wabe: Gwamnan APC da ake tunanin zai sauya sheka yayi zazzaga

An samu wani Gwamnan APC ya kuma sauke Kwamishinonin sa

Sakataren Gwamnatin Jihar ta Benuwai Farfesa Anthony Ijoho ya tabbatar da cewa Mai Girma Gwamna Samuel Ortom ya sallami wasu Kwamishinonin sa da kuma masu ba sa shawara wajen tafiyar da sha’anin mulkin Jihar.

Kwamishinoni 4 kacal aka bari a Gwamnatin Ortom wadanda su ka hada da: Kwamishinan Shari’a Mista Michael Gusa, sai kuma Farfesa Dennis Ityavyar wanda shi ne Kwamishinan Ilmi da kimiyya da fasaha na Gwamnatin Jihar.

KU KARANTA: Sau 38 ana rufe ni a gidan yari saboda Buhari - Galadima

Sakataren Gwamantin Jihar Anthony Ijoho ya kuma bayyana mana cewa ba a kori Kwamishinan kudi David Olufu daga kujeran sa ba. Haka kuma Bernand Unenge na nan a matsayin sa na Kwamishinan ma’adanai na Jihar Benuwai.

Daga cikin masu ba Gwamnan shawara da ba a sallama ba akwai Dr Magdalyne Dura, Matthew Mnyam. Akwai kuma irin su Cif Ode Enyi, Thomas Anajav, da Tahav Agerzua. Sai kuma Joseph Odaudu. da kuma Laftanan Kanal Paul Hemba.

Dazu kun ji cewa akwai yiwuwar Gwamna Ortom ya bar Jam’iyyar APC saboda rikicin sa da Sanata George Akume. Kwanaki ma dai Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal da ake tunani zai bar APC ya kori Kwamishinonin sa kaf.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel