An hurowa Shugaban kasa Buhari wuta ya tsige Ministar Kudi Adeosun

An hurowa Shugaban kasa Buhari wuta ya tsige Ministar Kudi Adeosun

Labari ya zo mana cewa yanzu haka mutane sun fara kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige Ministar kudin kasar bayan zargin da aka rataya a wuyan ta na amfani da shaidar bogi.

Idan ba ku manta ba wata Jarida ta zargi Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun da amfani da shaidar tsallake hidimar kasa watau NYSC na bogi duk da cewa shekarun ta ba su zarce na yi wa kasa hidima ba a lokacin da ta gama karatu.

Har yanzu dai Ministar tayi tsit ba tace komai ba game da zargin. Hukumar NYSC da Fadar Shugaban kasa duk sun yi bakkam game da lamarin. Gbenga Olorunpomi wanda ke aiki da Gwamnan Jihar Kogi ya nemi Ministar ta ajiye mukamin na ta.

KU KARANTA: Abin da ya sa na ke sukar Buhari - Ahmad Gumi

Gimba Kakanda wanda Marubuci ne yayi kira ga Fadar Shugaban kasar ta dauki mataki game da wannan badakala. Farouk Kperogi ma ya koka da yadda aka nada irin su Kemi Adeosun Minista duk da lokacin da aka bata wajen kafa Gwamnati.

Femi Fani-Kayode wanda ya saba sukar Gwamnatin Buhari yace nada Kemi Adeosun Ministar kudi yana cikin abin da ya jefa kasar cikin matsin tattalin arziki. Doka tace dole sai mutum yana da takardar kammala NYSC ko wanin sa kafin a dauke sa aiki.

Kun ji labari cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yace babu wanda ya isa ya canza halin Shugaba Buhari don gani yake yi kowa Barawo ne a kasar. Babban Malamin yace Shugaba Buhari gani yake yi na kusa da shi ne kurum mutane kirki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng