Nigerian news All categories All tags
Kwamitin yakin neman sake zaben shugaba Buhari sun bazama neman kudin yakin zabe

Kwamitin yakin neman sake zaben shugaba Buhari sun bazama neman kudin yakin zabe

- Wannan karon babu kudi ga yakin neman zaben gwamnati mai ci

- Kuma duk Ministan da yayi amfani da ofis din zan garkame shi

- Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, hakan ta sanya kwamitin yakin sake zabarsa ya bazama neman tsaba

Cikin kwanaki wadanda ba su gaza 221 da fara babban zaben kasar nan, dakarun yakin neman zaben shugaba Muhammad Buhari sun bazama neman kudin da zai tallafi yakin neman zaben.

Bazamar ta su ta biyo bayan furucin da fadar shugaban kasa ta yi, akan ba zata yi amfani da dukiyar al'ummar kasar nan ba, wajen yakin neman zabe.

Kwamitin yakin neman sake zaben shugaba Buhari sun bazama neman kudin yakin zabe

Kwamitin yakin neman sake zaben shugaba Buhari sun bazama neman kudin yakin zabe

A wani al'amarin kuma sabuwar Jamiyyar ANN ta bayyana dalilanta na ficewa daga hadakar jamiyyun da suka hada kai domin kalubalantar shugaba Muhammad Buhari. Jamiyyar ta ANN wacce ta kunshi wasu fitattun yan kasar nan wadanda su ka hadar da Gbenga Olawepo-Hashim da Fela Durotoye, da Dr. Elishama Ideh sai kuma Dr. Thomas Wilson Ikubese.

KU KARANTA: Ba batun zuwa Madrid: Salah ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool

Daya daga cikin masu yakin neman zaben, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa "Al'amarin yana da wahala, domin fasalin yakin neman zaben da aka yi na rashin samar da kudi, akwai wahala a ciki"

Tun da farko dai Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayar da sanarwar nada Rotimi Amaechi a matsayin babban daraktan yakin neman zabensa, da kuma babban lauyan nan Festus Keyamo a matsayin kakakin kwamitin yakin neman zaben.

Jim kadan da wannan nadin ne, sai aka jiyo shugaban kasa yana bayyana cewa babu kudin da za'a yi yakin neman zabe, kuma bai yadda wani minista ya yi amfani da ofishinsa wajen samar da kudin yakin neman zaben.

A karshe majiyar ta bukaci da a sakaye sunansa inda ya kara da cewa "lamarin yana da matukar Wahala, domin shugaban ya gargadi ministocinsa akan yin amfani da kudin al'umma, kuma ya ce duk wanda ya sabawa wannan matakin to babu shakka zai bakunci gidan yari"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel