Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari dauka yake yi kowa Barowa ne a Najeriya – Sheikh Gumi

Shugaba Buhari dauka yake yi kowa Barowa ne a Najeriya – Sheikh Gumi

Sheikh Ahmad Gumi wanda fitaccen Malamin addini ne a kasar nan a wata doguwar hira da yayi da Jaridar Punch ya bayyana cewa Shugaban kasa Buhari ya raba kan Jama’ar kasar.

Shugaba Buhari dauka yake yi kowa Barowa ne a Najeriya – Sheikh Gumi

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yace Buhari ya raba kan al'umma

Babban Malamin na Fikuhun Musulunci yace zuwan Shugaba Buhari ya farraka al’ummar Najeriya. Sheikh Ahmad Gumi yace ba Shugaba Buhari shawara ka da ya karbi mulkin kasar nan bayan Jonathan yayi mulki ba.

Shehin Malamin addinin yace ‘Yan kasar dai sun saduda da Gwamnatin Buhari. Gumi yace Shugaba Muhammadu Buhari ya maida hankalin sa kan abin da za a iya gyarawa nan gaba wanda hakan ya maida kasar baya.

KU KARANTA: Gwamnan Benuwe zai fice daga Jam'iyyar APC

Ahmad Gumi yace Jama’a su na jin tsoron sukar Gwamnatin Buhari domin gudun a hada su da Hukumar EFCC. Malamin yace hakan dai bat sarin farar hula bane kuma ya godewa Allah bai hada komai da Gwamnati ba.

Malamin Musuluncin ya nuna cewa har binciken Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da ake yi da zargin fashi da makami a Garin Offa siyasa ce. A dalilin haka ne Ahmad Gumi yace Gwamnatin Jonathan ta fi ta Buhari.

Sheikh Gumi yace babu wanda ya isa ya canza halin Shugaba Buhari don gani yake yi kowa Barawo ne a kasar nan. Malamin yace Shugaba Buhari gani yake yi na kusa da shi ne kurum mutanen kirki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel