Nigerian news All categories All tags
Duk da Buhari ya ba Abiola girman GFCR har yanzu akwai sauran aiki a gaban sa

Duk da Buhari ya ba Abiola girman GFCR har yanzu akwai sauran aiki a gaban sa

Mun samu labari cewa ‘daya daga cikin ‘Ya ‘yan Marigayi babban Lauya Gani Fawahemi mai suna Mohammed Fawahemi da wata Kungiya ta Arewa sun yi magana game da Marigayi MKO Abiola wanda ya lashe zaben shekarar 1993 lokacin IBB.

Wani na kusa da Marigayi Abiola mai suna Olawale yace sai da Abiola ya tambayi Shugaban kasa a lokacin Janar Babangida ko zai mika masa mulki idan yaci zabe. Sai dai IBB yayi haka ne kurum don ya zauna da su Shehu ‘Yaradua da Atiku lafiya.

KU KARANTA:

Olawale yace da farko dai Abiola bai da niyyar takarar Shugaban kasa a zaben. Sai dai IBB ne ya tunzara Abiola har kusan 3 cewa ya nemi Shugaban kasa. Sai dai kuma da Abiola ya kama hanyar lashe zaben, Gwamnatin Babangida ta taka masa burki.

Kungiyar ta Matasan Arewa AYCF ta nuna cewa lallai akwai bukatar a biya Marigayi tsohon ‘Dan siyasar kudin da yake bin Gwamnatin Tarayya. Kungiyar tace ba don Janar Ibrahim Babangida ya soke zaben 1993 da Abiola yayi mulkin kasar.

Mohammed Fawahemi shi ma yayi jawabi ne wajen bikin cika shekaru 20 da rashin Marigayi MKO Abiola. Kungiyar AYCF tace duk da cewa an karrama Abiola kwanaki akwai bukatar a biya Iyalan sa hakokin da yake bin Gwamnatin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel