Matsalar rashin tsaron jihar Zamfara ya rutsa da wani Dagaci, ‘yan bindiga sun aika shi barzahu

Matsalar rashin tsaron jihar Zamfara ya rutsa da wani Dagaci, ‘yan bindiga sun aika shi barzahu

- Harkar tsaro na cigaba da tabarbarewa a jihar Zamfara

- Irin wannan matsalar tsaron ce kuma ta lakume rayuwar wani basaren gargajiya jiya

- Har yanzu dai ba'a samu rahotan wadanda suka aikata mugun aiki ba

Wasu yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kashe Hakimin Kucheri, Alhaji Ibrahim Madawaki a lokacin da ya ke zaune a kofar gidansa da ke karamar hukumar tsafe da ke jihar Zamfara.

Matsalar rashin tsaron jihar Zamfara ya rutsa da wani Dagaci, ‘yan bindiga sun aika shi barzahu

Matsalar rashin tsaron jihar Zamfara ya rutsa da wani Dagaci, ‘yan bindiga sun aika shi barzahu

Wasu wadanda abin ya faru akan idonsu, sun bayyana cewa yan bindigar sun zo ne akan Babur, kuma suna zuwa su ka fara harbe-harbe kafin daga bisani su harharbi dagacin.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, in da jim kadan da faruwar lamarin ya bayyana cewa, jami'ansu sun garzaya, domin kare yin sata a gidan mamaci.

KU KARANTA: Wani Jami'in karbar haraji ya kashe wani magini ta hanyar amfani da Zoben tsafi

Ya kuma bayyana cewa kawo yanzu kwamishinan 'yan sandan jihar ta Zamfara Mr Kenneth Ebrimson, ya bayar da umarni da'a zurfafa bincike domin a gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

A karshe ya bukaci mutane da su kai rahoton dukkannin wani motsi da ba su yarda da shi ba, domin hakan zai taimaka wajen kawar da aikin ta'addanci da ya addabi jihar ta Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel