Nigerian news All categories All tags
Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da bada hadin kai wajen yaƙar cin hanci da rashawa

Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da bada hadin kai wajen yaƙar cin hanci da rashawa

- Yaki da cin hanci da rashawa ba yaki ne na shugaban kasa kadai ba

- Shugaba Buhari yayi kira ga 'yan Najeriya da su shigo a yi da su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi 'yan Najeriya da su cigaba da bada hadin kai wajen yaki da cin-hanci da rashawa da gwamnatinsa ke yi. Buhari ya yi wannan kira ne a ranar Asabar a Abuja, yayin bikin bude wani littafi da tsohon Ministan fasaha da Ƙere-ƙere manjo-Janar Sam Momah ya wallafa.

Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da bada hadin kai wajen yaƙar cin hanci da rashawa

Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da bada hadin kai wajen yaƙar cin hanci da rashawa

Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa an yi bikin kaddamar da littafin ne mai suna “Restructuring Nigeria beyond Oil’’, “Pulling Nigeria off the Brink’, domin taya mawallafin murnar cika shekaru 75 da haihuwa.

Buhari ya bayyana marubucin a matsayin mutumin da ke san ganin an kawo karshen cin-hanci da rashawa musamman ta hanyar rubuce-rubucensa, da kuma ganin an kare martabar Najeriya da bawa kowa 'yancinsa.

KU KARANTA: Rikicin APC - Gwamnoni da Ministoci zasu bawa Buhari mamaki - Galadima

Shubagan kasar wanda ya samu wakilcin zababben Sakataren ilimin bai daya na kasa (UBEC), Dakta Hamid Bobboyi ya shaidawa yan Najeriya cewa ya kamata kowa ya bada hadin kai don ganin an kawo karshen cin-hanci da rashawa a kasar nan.

A lokacin taya mawallafin murnar cika shekaru 75 da haihuwa, shugaba Buhari ya bayyana marubucin a matsayin dan kasa nagari, wanda ya yiwa kasarsa hidima matuka don ganin ta cigaba ta fannoni daban-daban.

Ya ce marubucin ya kasance mai son cigaban kasa duk da cewa ya yi ritaya daga aiki amma hakan bai hana shi yin Rubuce-rubuce tare da jawo hankali dangane da wasu matsaloli ba.

Shi daga bangarensa, marubucin cewa yayi bashi da wani buri da yake da shi a yanzu wanda ya wuce kawo mafita dangane da matsalolin Najeriya domin ganin an haifi ɗa mai ido a nan gaba, kuma zai yi hakan ne ta hanyar rubuce-rubucensa.

Marubucin ya kara da cewa ya wallafa littafin farko ne domin sanin halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki musamman ta yadda aka dogara akan man fetur sannan a daya littafin kuma ya kawo yadda za a shawo kan matsalar tattalin arzikin tare da dogara da kai ba tare da man fetur ba.

Taron bikin kara shekara nasa ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma tsofaffin sojojin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel