Nigerian news All categories All tags
Dalilin da yasa nake sukar shugaba Buhari – Sheikh Gumi

Dalilin da yasa nake sukar shugaba Buhari – Sheikh Gumi

Sheikh Dakta Abubakar Gumi ba bako bane a wajen sukar shugabannin dake kan mulkin Najeriya, kamar yadda jama’a suka sani. Tun bayan hawan shugaba Buhari, Sheikh Gumi ke sukar manufofi da tsare-taren gwamnatinsa kamar yadda ya yiwa tsohon shugaban kasa Jonathan.

A wata hira da ya yi da jaridar Punch, Sheikh Gumi, ya bayyana cewar yana sukar gwamnati ne yayin da ya kasance matsalolin da ta kawo sun fi nasarar da ta samu yawa.

Sheikh Gumi ya kara da cewa, “na soki gwamnatin baya ta Jonathan musamman lokacin da asarar rayuka, sakamakon rikicin Boko Haram, ya yi yawa. Amma a wancan lokacin an samu cigaba mai yawa a arewacin Najeriya; an gina jami’o’i, an gina makarantu domin almajirai da layukan jirgin kasa, hatta tattalin arzikin Najeriya a wancan lokacin ya fi na yanzu.

Dalilin da yasa nake sukar shugaba Buhari – Sheikh Gumi

Sheikh Ahmad Gumi

Amma yanzu bayan kashe-kashen rayuka da matsin tattalin arziki, gwamnatin ba ta nuna damuwarta da halin da jama’a ke ciki. Idan maganar tsaro ma ake yi, gara gwamnatin Jonatahan da ta Buhari.

DUBA WANNAN: Badakalar cin hancin N15bn: Kotu ta tsayar da ranar yankewa Bafarawa hukunci

Da aka tambaye shi ko mai yasa a matsayinsa na malamin addini daga arewa yake yawan sukar shugaba Buhari, sai y ace, “ba maganar addini ba ce, Magana ce ta fadin gaskiya. Mutanen arewa basa son a taba Buhari, suna ganinsa kamar wani ma’asumi da baya aikata kuskure. Tsarin sarautar gargajiya ne ya kashe tunani da kwakwalwar mutane arewa, domin a tsarin masarauta ba zaka soki shugaba ba. Kai, ko sutura ba zaka saka mai kyau da tafi ta shugaba ba. Wannan dalilin ya saka ‘yan arewa ke yiwa Buhari makauniyar biyayya har ta kai ga suna ganin shi tamkar ba mutum ba,” a cewar Sheikh Gumi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel