Nigerian news All categories All tags
Yunkurin tsayawa takarar shugaban kasan Bukola Saraki ta haifar da rarrabuwar kai a R-APC

Yunkurin tsayawa takarar shugaban kasan Bukola Saraki ta haifar da rarrabuwar kai a R-APC

- Da yiwuwar Saraki zai kara da Tambuwal da Kwankwaso da Makarfi da Atiku don zama dan takarar shugaban kasa

- Tsoffin yan cikin PDP na ganin su suka fi cancanta a basu tikitin takara ba baki ‘yan kome ba

- Obasanjo kuma zai goyi bayan duk wanda PDP ta tsayar ko da kuwa Atiku ne

Yanzu haka dai shirye-shirye sun fara kankama na yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ke yi amma a jam’iyyar PDP.

Yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa Bukola Saraki ta haifar da rarrabuwar kai a R-APC

Yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa Bukola Saraki ta haifar da rarrabuwar kai a R-APC

Wannan batu dai na fitowa ne daga bakin wata majiya mai tushe ta kusa da shugaban majalisar, majiyar ta bayyana cewa yunkurin ya samo asali ne cikin awanni 24 bayan da kotun daukaka kara ta wanke shi daga zargin da ake masa, kuma takarar zata kasance ne a watan Agusta mai kamawa.

Sakin wannan labara ke da wuya ne kuma aka fara samun rarrabuwar kai a gidajen magoya bayan gwamna Aminu Waziri Tambuwal da kuma ‘yan gidan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wadanda su ne jigon tsagin r-APC.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa Tambuwal da Kwankwaso na daga cikin masu zawarcin kujerar shugabancin kasar nan a jam’iyyar adawa bayan da suka tabbatar ba zasu iya karawa da shugaba Buhari a zaben cikin gida na jam’iyyar APC ba.

Bayyana wanke shi da kotu ta yi ne (Saraki) magoya bayansa suka matsa lallai-lallai da ya fito takarar shugabancin kasar nan bayan kammala tuntuba da su kayi.

To amma sai dai idan ya ce zai nemi takarar hakan zai sanya a sake lale a cikin tsagen na rAPC a gabannin zabe mai zuwa.

Ita dai rAPC ta samo asali ne bayan da wasu jigogi a jam’iyyar ta APC suka kafa ta ranar Larabar da ta gabata bisa dalilin rashin ba su kulawar da ta kamata da kuma gaza zuwa inda ake zato da gwamnatin ta yi.

KU KARANTA: An bankado wasu masu shirye-shiryen dakatar da shugaba Buhari takara saboda tsufansa

Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya kai ziyara jihar Rivers domin kaddamar da wasu aiyuka da gwamnan PDP Nyesom Wike yayi, wannan tafiya ne bisa dalilin fara shirye-shiryen komawarsa jam’iyyar PDP a shekara mai zuwa.

Wannan yunkurin tsayawa takara da Saraki ke shirin farawa dai ya kuma jefa magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atku Abubakar cikin rudani, kasancewar “Ya saba da yarjejeniyar da shuwagabannin biyu suka cimma a gabashin Najeriya.” A cewar wani makusancin ‘yan gidan Atikun.

Saraki dai na jin cewa bai cancanci muzanta shi da akai a gaban kotun da’ar ma’aikata ba, ga kuma shafa mishi kashin kaji da babban sufeton ‘yan sanda na kasa yake kokarin yi dangane cewa yana da hannu a cikin fashin da aka yi na Offa.

To amma sai dai a cikin jam’iyyar PDP ma yanzu haka sun nuna rashin amincewarsu da a baiwa wani bare da ya yo kome cikin jam’iyyar tikiti, ‘yan PDP suna ganin tabbas a cikin ‘yan jam’iyyar na halak malak ne da ba su taba rawa ba suka cancanta a baiwa tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019.

Amma sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma wasu jam’iyyu 30 sun amince zasu marawa duk wani dan takara da PDP ta tsayar ko da kuwa Atiku Abubakar ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel