Nigerian news All categories All tags
Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki

Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki

A yau Asabar, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce tabbas sashin shari'a na Najeriya yana aikinsa duk da cewa akwai wasu kaluballe da yake fuskanta, ya kuma kara da cewa bai dace a bari wani mahaluki ya kawo cikas ga sashin ba.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a yayin da yake tsokaci kan hukuncin da kotun ta yanke na wanke shugaban majalisa Bukola Saraki daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa a wata sanarwa da ta fito daga mataimakinsa na musamman a fanin yadda labarai, Garba Shehu.

A jiya Juma'a 6 ga watan Yuli ne kotun koli da wanke Bukola Saraki daga tuhumarsa da kotun da'ar ma'aikata tayi na yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki

Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki

DUBA WANNAN: Dokar ta baci: 'Yan PDP zasu garzaya kotu don hana Buhari kwace kadarorinsu

Shugaba Buhari yace: "So da yawa naga yadda wasu mutane ko kungiyoyi kanyi kokarin kawo cikas ga shari'a a tunanin hakan ne zai tsiratar dasu a maimakon juriya da bin doka wajen jadada gaskiyarsu.

"Amma a shari'ar shugaban majalisa Bukola Saraki, na ga yadda ya yi hakuri kuma ya jure dukkan wahalhalun da ke tattare da shari'a kuma daga karshe kotu mafi daraja a kasa ta ce bashi da laifi.

"Abinda nayi kenan har sau uku a kotu a lokacin da aka zalunce ni kan sakamakon zabe har sai da Allah ya bani nasara a karo na hudu.

Yadda shugaban majalisar dattawar ya yi hakuri da shari'ar tun daga kananan kotunaa har zuwa kotun koli babban darasi ne ga yan Najeriya da ya kamata suyi koyi dashi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ruwaito cewa Kotun kolin ta tabbatar da hukuncin da kotun da'ar ma'aikata ta yanke kan shari'ar Saraki inda ta wanke shi daga dukkan laifuka 18.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel