Nigerian news All categories All tags
ICPC ta bude bincike kan Ministocin Buhari cikin batun kwangilar aikin jiragen kasa

ICPC ta bude bincike kan Ministocin Buhari cikin batun kwangilar aikin jiragen kasa

- ICPC na binciken almundahana da akayi da sunan daukar nauyin karatu na railway wanda wasu wai jiga jigan jami'an gwamnati suka yi

- Majiyar mu ta samo mana labarin yadda wasu ministoci da manyan jami'an gwamnati wai suka waskar da kudin tallafin karatun wasu 'yan Najeriya

ICPC ta bude bincike kan Ministocin Buhari cikin batun kwangilar aikin jiragen kasa

ICPC ta bude bincike kan Ministocin Buhari cikin batun kwangilar aikin jiragen kasa

Kamfanin Chanis, Civil Engineering Construction Corporation, na kananan yan Najeriya domin karatun digiri a fannin kimiyya jiragen kasa a Chana.

Majiyar mu ta ruwaito cewa manyan jami'an gwamnatin da suka nemar wa daliban hanyar shiga jerin wadanda za a tallafa ma wa sun hada da Rotimi Amaechi, Adebayo Shittu, Abubakar Badaru.

Daliban da sunayen su suke takardun kamfanin kadai aka kira intabiyu a ofishin CCECC a Abuja. Duk sunayen daliban na tare da wanda yayi mishi hanyar samun shiga jerin wadanda za a tallafa ma wa. Maimakon ace an zabo daga kowa ba tare da uban gida ba.

Dalibai da yawa da suka halarci intabiyu din da babu sunan su a jerin alfarmar an hana su shiga gurin.

DUBA WANNAN: Amurka da Iran na sa'insa kan makamashi

Bayan wannan rahoton ne 'yan Najeriya suka bukaci binciken jami'an da suka killace damar domin su da wadanda suka sani kacal.

ICPC ta gayyaci CCECC domin amsa tambayoyi inda Sabiu Zakari ya wakilce su.

Sakataren ma'aikatar sufuri ne ya aika da wasiku ga ma'aikatu cewa su bada sunayen mutanen su.

Sakataren dai zai bayyana ne a ranar litinin ko talata, Inji majiyar mu.

Ministocin da jami'an gwamnatin suma zasu amsa nasu tambayoyin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel