Nigerian news All categories All tags
Daliba ta rataye kanta a makarantar da dalibai 10 suka rataye kansu a shekaru biyu

Daliba ta rataye kanta a makarantar da dalibai 10 suka rataye kansu a shekaru biyu

- An gano gawar wata daliba 'yar Najeriya, Omojola Ogundipe, dake karatu a jami'ar Bristol dake Ingila

- Binciken da yan sanda suka gudanar ya nuna cewa ta ita ta kashe kanta

- Wannan shine karo na 11 da dalibai ke kashe kansu a cikin shekaru biyu da suka gabata a jami'ar

Muna samu rahoton cewa wata dalibar jami'ar Bristol mai shekaru 20, Omojola Ogundipe, ta kashe kanta a dakin wani Otel dake garin Cardiff.

Ma'aikata a Citrus Otel dake Cardiff ne suka gano gawarta a sagale a dakinta bayan ta wuce adadin kwanakin data biya a Otel din kamar yadda The Sun UK ta ruwaito.

An gano cewa marigayiyar ta biya kudin dakin tun makonni uku da suka gabata.

Daliba ta rataye kanta a makarantar da dalibai 10 suka rataye kansu a shekaru biyu

Daliba ta rataye kanta a makarantar da dalibai 10 suka rataye kansu a shekaru biyu

DUBA WANNAN: An fara bincike kan hukumar kwallon kafa ta kasa NFF kan badakalar miliyoyi

Legit.ng ta tattaro cewa marigayiyar tana aji na biyu na inda take karantar nazarin tattalin arziki a jami'ar Bristol kuma tana daya daga cikin mawakan Choir a cocin jami'ar.

Ogundipe wanda aka bayyana a matsayin mai fara'a da walwala itace daliba na 11 da ta kashe kanta cikin shekaru biyu da suka gabata a jami'ar.

Wata kotu da ke Pontypridd ta gudanar da bincike kan rasuwar dalibar kuma daga baya aka bayyana cewa babu wani da ya shiga dakinta kuma bata fita zuwa ko'ina ba wanda hakan na nufin ita ta kashe kanta.

A wata sanarwa da mahaifinta ya bayar, Kurle Ogundipe ya ce ya yiwa diyarsa ganin karshe a ranar 11 ga watan Mayu lokacin da ta dawo gida hutun karshen mako. Ya kuma ce tana cike fa fara'a kamar yadda ta saba kasancewa.

Ya kuma ce bashi da masaniya a kan wata rashin lafiya da ke damun diyarsa kuma baya tunanin tana fama da wata damuya ko tashin hankali.

Sai dai wata kawar marigayiyar, Hannah Agbeyegbe, ta shaidawa kotu cewa Omojola ta fada mata cewa "fama da damuwa kuma tana tunanin kashe kanta".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel