Nigerian news All categories All tags
An fara bincike kan hukumar kwallon kafa ta kasa NFF kan badakalar miliyoyi

An fara bincike kan hukumar kwallon kafa ta kasa NFF kan badakalar miliyoyi

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta fara bincike a kan jami'an hukumar kwallon kafa na kasa (NFF) da aka sallama daga aiki.

Jami'an sun da tsohon shugaban hukumar Amaju Pinnick da mataimakinsa, Seyi Akinwumi da ciyaman din kwamitin gasar wasanni, Shehu Dikko da Sakatare Janar, Muhammad Sanusi da kuma mamba mai suna Ahmed Yusuf Fresh.

Fara binciken ya biyo bayan karar da tsohon mai horas da yan wasan Najeriya, James Peters ya shigar wa EFCC inda ya yi ikirarin cewa an tabka mummunar sata a hukumar kwallon kafar kamar yadda takardan ta isa ga EFCC a ranar 4 ga watan Mayun 2018.

An fara bincike kan hukumar kwallon kafa ta kasa NFF kan badakalar miliyoyi

An fara bincike kan hukumar kwallon kafa ta kasa NFF kan badakalar miliyoyi

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sunyi wa Fulani mummunar ta'asa a jihar Taraba

A cikin takardar karar, Peters wanda ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa wasanni da dama da su kayi nasara ya bukaci EFCC ta gudanar da cikaken bincike a kan 'sata' da rashawa da yace an tafka a karkashin Amaju Pinnick da Dr. Muhammadu Sanusi da Seyi Akinwumi da Mallam Shehu Dikko da Alhaji Ahmed Yusuf Fresh.

Tsohon mai bayar da horon kuma ya ce anyi amfani da wata kamfani mai suna Financial Derivatives Ltd wanda tsohon shugaban NFF Amaju Pinnick ya zabo musamman don karkatar da kudade daga asusun hukumar dake babban bankin Najeriya CBN.

Har ila yau, yace tsaffin jami'an sunyi amfani da wata kamfani mai suna Mediterranean Sports Limited mallakin Mallam Shehu Dikko wanda shine tsohon mataimakin shugaban hukumar kuma wanda aka daura wa alhakin kulawa da shirya gasar kwallon kafa na kungiyoyin Najeriya.

Peters ya kuma ce shugabanin basu taba bayyana kudaden da kamfanoni masu daukan nauyin wasar kwallon kafar ke bayarwa ba. Ya yi kira a bi didigin dukkan kudaden sallamar aiki da fansho na tsaffin ma'aikatan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel