Nigerian news All categories All tags
Rikicin APC - Gwamnoni da Ministoci zasu bawa Buhari mamaki - Galadima

Rikicin APC - Gwamnoni da Ministoci zasu bawa Buhari mamaki - Galadima

Kwanaki biyu bayan wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar APC sun ware kansu daga uwar jam'iyyar saboda rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da harkokin jam'iyyar, shugaban sabuwar APC din, Buba Galadima ya furta cewa wani abinda zai razaka jam'iyyar APC na nan tafe.

Galadima ya yi zargin cewa mutane da yawa da ke kusa da shugaba Muhammadu Buhari suna da hannu dumu-dumu cikin rashawa.

A hirar da ya yi da Saturday Sun, Buba wanda dan aslin jihar Yobe ne kuma tsohon aminin shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai wasu Gwamnoni da Ministoci masu ci yanzu da zasu shigo sabuwar jam'iyyar ta APC.

Rikicin APC - Gwamnoni da Ministoci zasu bawa Buhari mamaki - Galadima

Rikicin APC - Gwamnoni da Ministoci zasu bawa Buhari mamaki - Galadima

DUBA WANNAN: Dokar ta baci: 'Yan PDP zasu garzaya kotu don hana Buhari kwace kadarorinsu

Ya bayar da misali da yadda wasu kusoshin jam'iyyar ta APC a jihar Kwara suka fice daga jam'iyyar inda ya kara da cewa za'a samu karin masu ficewa daga wasu jihohin. Sai dai bai fadi rannan da wannan abin mamamkin zai faru ba.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa shugaban na sabuwar APC wanda suka hada kai da 'yan bangaren sabuwar PDP yace suna da karfin da yawa a majalisar tarayya da za su iya tsige shugaba Muhammadu Buhari idan hakan ta kama.

Galadima ya mayar da martani kan kalaman shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole inda ya yi ikirarin cewa mutanen dake da rAPC basu da wani muhimmanci, yace wanda ke adawa dasu ne basu da nagarta.

Injiniya Galadima wanda yana cikin amintattun jam'iyyar APC kuma tsohon jigo a jam'iyyar CPC, ya yi kira ga 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata su goyi bayan sabuwar jam'iyyar nasu. Jam'iyyar ta rAPC da aka kafa kwananan ne dan nufin ceto 'yan Najeriya daga kangin da suke shiga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel