Nigerian news All categories All tags
Amurka ta kara aiko wa gwamnatin Tarayya biliyoyi don yaki da cutar kanjamau

Amurka ta kara aiko wa gwamnatin Tarayya biliyoyi don yaki da cutar kanjamau

- Amurka ta baiwa Najeriya dala biliyan 5 da doriya cikin shekaru 15 daga 2003

- Shirin PEPFAR wanda shugaba Bush ya kaddamar ya kawar da miyagun annoba a Afirka

- Ya zuwa yanzu dai wannan shiri ne ya hana cutar yaduwa tsakanin al'umma da kisan masu ita

Amurka ta kara aiko wa gwamnatin Tarayya biliyoyi don yaki da cutar kanjamau

Amurka ta kara aiko wa gwamnatin Tarayya biliyoyi don yaki da cutar kanjamau

A bikin cikar shirin PEPFAR da ake yi yanzu haka a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, mukaddashin shirin Amurkar a Najeriya, Mista Young, yace a shekaru 15, kasar Najeriya ta sami tallafin dala biliyan biyar don yakar kanjamau.

A cewarsa dai, tun da aka fara shirin don tallafawa Afirka, Najeriya da sauran kasashe sun yaki cutar wadda tafi karfin gwamnati ta iya kawar da ita ita kadai.

Shirin dai shi ya hana cutar yaduwa da sauri, ya kuma kawo saukin samar da magunguna ga wadanda cutar tayi wa tu'annati tare da kare yara kamuwa da ita, ko a ciki ko a wajen haihuwa.

DUBA WANNAN: PDP na taya rAPC murnar 'lashe zabe'

A yanzu dai, kanjamau ta rage yaduwa amma dai da sauran rina a kaba, domin kuwa, a Najeriya ana sa rai akalla mutum 3m neke dauke da cutar, kuma basu gaya wa jama'a sai dai su yi kokarin yada ta tsakanin al'umma musamman mata ko mazansu na aure.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel