Nigerian news All categories All tags
Zaben gwamnan Ekiti: Shure-shuren 'mutuwa' gwamna Fayose keyi - Oshiomole

Zaben gwamnan Ekiti: Shure-shuren 'mutuwa' gwamna Fayose keyi - Oshiomole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomole yace gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti da sauran yan jami'iyyarsa ta PDP sun karaya kuma suna shure-shuren 'mutuwa' ne bayan sun hango cewa ba za suyi nasara ba.

Oshimole ya fadi wannan magana ce a yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam'iyyar na kasa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a.

Ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ra dakile dukkan hanyoyin magudi da gwamnan ya dagora dashi a baya.

Zaben gwamnan Ekiti: Shure-shuren mutuwa a siyansance gwamna Fayose keyi - Oshiomole

Zaben gwamnan Ekiti: Shure-shuren mutuwa a siyansance gwamna Fayose keyi - Oshiomole

DUBA WANNAN: Muna da rinjaye da zamu iya tsige Buhari a majalisa - rAPC

Ya cigaba da cewa Fayose yana tsoro ganin cewa ma'aikatan gwamnati da malaman makarantu na jihar Ekiti da iyalansu baza su jefa masa kuri'a ba.

Ya kuma ce har yanzu gwamnan bai biya ma'aikatan jihar albashinsu na shekara guda ba duk da irin kudaden da tallafin da gwamnatin tarayya ta raba wa gwamnonin jihohi a baya.

Oshiomole ya kuma bayyana cewa a lokacin babban zaben kasa na shekarar 2015, gwamnatin PDP ta hana su sauka a filin saukan jiragen sama na jihar ta Ekiti kawai don a dagula musu lissafi.

Ya ce jam'iyyar APC ba za ta aikata irin wannan abin ba saboda tayi imani da biyaya ga doka da oda da kuma demokradiyya mai tsafta.

A bangarensu, jam'iyyar PDP ta kallubalanci dan takarar APC kuma tsohon gwamnan jihar, Dr. Kayode Fayemi ya nuna wa al'umma ayyukan da ya yi da bashin N25 biliyan da ya karbo a zamanin mulkinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel