Nigerian news All categories All tags
Abin nema ya samu wa PDP ta aika sako ga sabuwar jam'iyyar APC

Abin nema ya samu wa PDP ta aika sako ga sabuwar jam'iyyar APC

- Jam'iyyar PDP na murna da yagewar takwararta ta APC

- A 2013 ma anyi haka inda aka yayyaga PDP gabanin zabukan 2015

- Kujerar shugaba Buhari na fuskantar barazana

Abin nema ya samu PDP ta aika sako ga sabuwar jam'iyyar APC

Abin nema ya samu PDP ta aika sako ga sabuwar jam'iyyar APC

Jam'iyyar Adawa ta PDP, wadda ta sha kaye a 2015, yanzu ita ke darawa saboda irin diramar da ake tafkawa a APC, wadda ita ma yanzu ta rabe biyu, kuma kwanne na ikirarin lallai dasu za'a dama kuma su ke da jam'iyyar a Abuja.

Sakon da jam'iyyar PDPn ta aikewa jam'iyya APC dai ya fito ne daga reshen jihar Edo, inda Adams Oshiohole ya gama gwamna a kwanan nan kafin ya zama shugaban APCn.

DUBA WANNAN: Buhari yace zai kama 'yan siyasa masu tayar da zaune tsaye

Sakon na taya bangaren Buba Galadima murna ne, saboda wai namijin kokari da suka yi domin tsage gaskiya da ballowa daga 'zaluncin' APC.

Shi kuwa Adams Oshiomhole, cewa yayi, zasu murkushe bangaren adawa na cikin gida, ba zasu sassauta musu ba.

A 2013 dai da haka aka fara wa PDP kafin aka sami damar kada ta a zabe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel