Nigerian news All categories All tags
Zamu murkushe masu kokarin yaga jam'iyyar APC - Oshiomole

Zamu murkushe masu kokarin yaga jam'iyyar APC - Oshiomole

Sabin shugaban jam'iyyar APC, Kwamared Adams Oshiomole ya ce jam'iyyar zata murkushe 'yan a tawayye dake kiran kansu sabuwar APC (rAPC) ta hanyar gabatar da dalilai gamsasu.

Sai dai shugaban sabuwar APC, Injiniya Buba Galadima yace sabuwar APC din tana da rinjaye da zata iya tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan sun ga dama.

A yayin da yake jawabi ga wasu mutane da suka bayyana kansu a matsayin shugabain tsohuwar jam'iyyar CPC da su kace basu tare da rAPC, Oshiomole ya amince akwai wasu kallubalai a APC amma yayi alkawarin za'a warware su.

Zamu murkushe masu kokarin yaga jam'iyyar APC - Oshiomole

Zamu murkushe masu kokarin yaga jam'iyyar APC - Oshiomole

DUBA WANNAN: Hatsarin tankar dakon man fetur 5 mafi muni da suka faru a 2018

Ya ce bisa ga dukkan alamu wadanda suka kafa sabuwar APC suna da wata akida daban wanda ta bambanta da na APC shiyasa suka ware kansu.

Ya tabbatar wa tawagar cewa shugabanin jam'iyyar na APC zasu cigaba da tattaunawa da wadanda ke da matsaloli a jam'iyyar don ganin an warware su.

Shugaban tawagar, Umar Shuaibu kuma ciyaman din tsohuwar jam'iyyar CPC na jihar Neja ya nisanta kansa da tsaffin ciyamomin CPC daga tafiyar ta rAPC.

A jawabinsa, tsohon ciyaman din CPC a Jihar Benue, Noah Mark Dickson wanda aka lissafo sunansa cikin sabbin shugabanin rAPC yace 'yan kungiyar basu tuntube shi ba kafin suka rubuta sunansa. Shima na nisanta kansa daga kungiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel