Nigerian news All categories All tags
Dokar ta baci: 'Yan PDP zasu garzaya kotu don hana Buhari kwace kadarorinsu

Dokar ta baci: 'Yan PDP zasu garzaya kotu don hana Buhari kwace kadarorinsu

Jam'iyyar PDP ta ce bayyana cewa zata garzaya kotu don dakatar da dokar ta baci da shugaban kasa ya rattaba hannu a kai jiya wadda zata bawa gwamnati damar adana duk wata dukiya da aka sameta ta hanyar cin hanci kuma gwamnati ta kwace ta.

A sanarwan da sakataran yadda labarai na PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar a yau Juma'a, yace dokar ta sabawa ka'ida kuma ta ci karo ta kundin tsarin mulki bugu da kari hanya ce da zata kai Najeriya ga mulkin kama-karya.

Dokar ta baci: 'Yan PDP zasu garzaya kotu don hana Buhari kwace kadarorinsu

Dokar ta baci: 'Yan PDP zasu garzaya kotu don hana Buhari kwace kadarorinsu

Jam'iyyar ta PDP ta ce kirkiro dokar kwace kadarorin rashin da'a ne ga kundin tsarin mulkin Najeriya ta shekarar 1999.

DUBA WANNAN: Muna da rinjaye da zamu iya tsige Buhari a majalisa - rAPC

"Lauyoyin mu sun fara shirye-shiryen maka gwamnatin tarayya a kotu saboda saba dokar da shugaban kasar ya yi saboda muna kishin yan Najeriya."

Jam'iyyar kuma tace babu wani sashi na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bawa shugaban kasa ikon kafa irin wannan dokar.

Kazalika, jami'iyyar ta adawa tayi ikirarin cewa shugaban kasan kawai ya kirkiri dokar ne saboda ya bawa kansa ikon da karfi wanda zai yi amfani dashi wajen musgunawa yan adawa da duk wasu masu wata ra'ayi da ba nasa ba.

Jam'iyyar tayi kira ga sashin shari'a na Najeriya da 'yan majalisar tarayya su tashi tsaye don ceto yan Najeriya ta hanyar kin amincewa da kafuwar dokar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel