Nigerian news All categories All tags
Hukumar 'yansanda ta kama 'yansandan da suka mammari lauya suka yankwana shi a bidiyo

Hukumar 'yansanda ta kama 'yansandan da suka mammari lauya suka yankwana shi a bidiyo

- An nuno su a bidiyo suna ta kia ma lauyan mari a cikn gidansa, suna cumuimuyarsa

- Dama dai SARS an san su da cin zarafin mutane ba kan doka ba

- Hukumar yansanda na kokarin kakkabe baragurbin jami'anta, wanda a iya cewa sun ma fi na kirkin yawa a halin yanzu a kasar nan

Hukumar 'yansanda ta kama 'yansandan da suka mammari lauya suka yankwana shi a bidiyo

Hukumar 'yansanda ta kama 'yansandan da suka mammari lauya suka yankwana shi a bidiyo

Hukumar yan sandan jihar Legas ta kama yan sanda biyu da ake zargi da barazana ga wani lauya, Olakunle Kareem.

Jami'in hulda da jama'a na yan sandan jihar, CSP Chike Oti, yace jami'in Dan sandan dake kula da Lion Building Division shima an tuhume shi akan abinda ya faru.

Kareem da shugaban shi, Oluyemi Olawore, babban lauya kuma abokin huldar Olawore & Co,... Sun samu yar hayaniya a ofishin su dake McCarthy Street, tsibirin Legas.

Olawore wanda aka ce shi ya gayyaci yan sandan daga cikin Lion Building Police Division, ya zargi Kareem da barazana da tsare shi.

Bidiyon abinda ya faru ya yadu a yanar gizo, wanda ke nuna yanda yan sandan biyu suka dinga wanke ma Kareem fuska da mari.

DUBA WANNAN: An kamo dansandan da ya kashe kopa, an koras daga aiki, kuma an kaishi kotu

Kareem da ya bukaci yan sandan su saurare shi, ya musa tsare shugaban shi da aka ce yayi, a yayin da daya daga cikin yan sandan ya shake shi tare da barazanar harbin shi a kafa.

Mai magana da yawun yan sandan yace an kama yan sandan saboda rashin iya aiki da suka gwada.

Yace "Wani bidiyon yan sandan dake barazana ga matashin lauya inda suke bukatar albashin shi ya jawo hankalin kwamishinan yan sandan jihar Legas, Edgal Imohimi wanda ya shirya masu bincike don su duba zargin."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel