Nigerian news All categories All tags
An damke mutane 5 game da kisan yan sanda 7 a Abuja

An damke mutane 5 game da kisan yan sanda 7 a Abuja

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa an damke mutane biyar da ake zargi da hannu cikin kisan yan sanda 7 a unguwar Galadimawa, babban birnin tarayya Abuja.

Kakakin hukumarr yan sanda, DCP Jimoh Moshood, ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambayoyi daga bakin manema labarai yau Juma’a a Sukeja, jihar Neja.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa yan bindiga a ranan Litinin sun hallaka jami’an yan sanda bakwai a shataletalen unguwar Galadimawa a cikin birnin tarayya Abuja.

Yace: “ A yanzu haka da nike muku magana, mun damke mutane biyar game da wannan hari kuma muna kan kamawa.”

“Za mu tabbatar da cewa duk wandanda ke da hannu cikin wannan mugun laifi sun shiga hannu,”.

KU KARANTA: Wannan Amarya ta rasu a daren ranan aurenta

Moshood ya kara da cewa sifeto janar na hukumar yan sanda ya bada umurnin cewa a biya iyalan yan sandan da suka rasa rayukansu alawus dinsu.

Kana ya umurci dukkan sassan tsaro su karfafa tsaro kuma ya hada jami’ai na musamman domin damke wadanda sukayi wannan abu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel