Nigerian news All categories All tags
PDP da Atiku sun yabi nasarar Saraki a kotun koli

PDP da Atiku sun yabi nasarar Saraki a kotun koli

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana hukuncin kotun koli da ta sallami karar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a matsayin tubalin adalci.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta saki ta hannun sakataren labaranta, Kola Ologbondiyan tace hukuncin kotun koli, ya kara tabbatar da aminci a bangaren shari’a musamman a karkashin gwamnatin zalunci.

Hakazalika, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a wata sanarwa da ya saki ta hannun kakakinsa yace a bayyane yake karara cewa tuhumar da ake yiwa shugaban majalisar dattawa a gaban kotun CCT ba komai bane face siyasa.

PDP da Atiku sun yabi nasarar Saraki a kotun koli

PDP da Atiku sun yabi nasarar Saraki a kotun koli

Ya yabama hukuncin kotun koli wacce ta wanke Saraki.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kakakin majalisar wakilai, Mista Yakubu Dogara ya taya shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki murnar nasarar da yayi a kotun koli a ranar Juma’a, 6 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotun koli ta wanke Bukola Saraki daga dukkan zargin da gwamnati ke masa

A wata sanarwa da Dogara ya fitar a ranar Juma’a a Abuja ta hannun mai ba shi shawara akan harkokin labarai, Mista Turaki Hassan, ya ce ya samu labarin hukuncin kotun koli cike da farin ciki.

Ya bayyana cewa hukuncin ya nuna amana a bangaren shari’a a lokacin da mutane basu yi tsammani ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel