Nigerian news All categories All tags
Korarren Farfesa yayi fira da 'yan jarida: Dalilin da yasa naso dalibar nan ta bani kanta

Korarren Farfesa yayi fira da 'yan jarida: Dalilin da yasa naso dalibar nan ta bani kanta

- An ji sakon hirarsu a waya sanda yake neman lalatar da ita

- Hukumar Jamia ta kore shi daga aiki kan iskancin nasa

- Yanzu yayi bayanin dalilansa na neman biyan bukata da ita

Korarren Farfesa yayi fira da 'yan jarida: Dalilin da yasa naso dalibar ta bani kanta

Korarren Farfesa yayi fira da 'yan jarida: Dalilin da yasa naso dalibar ta bani kanta

Farfesa Richard Akindele, korarren malamain jami'a da aka ji shi yana cinikin yadda zai sami kwanciya da wata yarinya sau biyar, kafin ya barta ta ci jarrabawa, ya ito yana kokarin kare kansa bayan da jami'ar OAU ta kore shi daga aiki.

Malamin tsumulmular da tattali, ya nemi budurwa Monica Osagie, da ta bashi hadin kai domin a cewarsa, sauran 'yan matan ma tuni sun bashi hadin kai, kamar yadda sakon muryar ya nuna.

Sai dai a kokarin kare kansa, yace ai so yayi wai ya gayyace ta ofishinsa domin ya tatsi bayanan da zasu sa ya kama ta da hujja.

DUBA WANNAN: Anyi mare-mare a gidan gwamnati

An dai san malaman makarantu da neman matan tsiya, inda su kuma dalibai da saurin bada kansu domin hayewa jarrabawa, wanda hakan ya sa har yanzu ko na'urar kalkileta ba'a kerawa a Najeriya, duk da miliyoyin dalibai da ake yayewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel