Nigerian news All categories All tags
Yaro dan shekara uku ya mutu a shadda

Yaro dan shekara uku ya mutu a shadda

Rahotanni sun kawo cewa wani dan karamin yaro mai shekaru uku a duniya ya hadu da ajalinsa bayan da ya fada cikin masai a kasar Afirka ta Kudu.

Yaron mai suna Omari Monono ya mutu ne a wani bandaki da ke wajen gidansu a lardin Limpopo, wurin da aka taba samun wani yaro mai sheharu biyar mai suna Micheal Komape ya mutu a shadda a shekarar 2014.

"Ina cikin matukar damuwa, ba na iya cin abinci, ba na iya bacci," a cewar mahaifiyar marigarin Kwena Monono.

"A kowane lokaci na ga wani abu da yarona yake so, sai zuciyata ta karaya sai kuma kuka ya zo mini."

Yaro dan shekara uku ya mutu a shadda

Yaro dan shekara uku ya mutu a shadda

Mahaifiyar yaron ta ce an fito da yaron daga cikin shadda a ranar Laraba ne da misalin karfe hudu agogon can, sa'o'i biyu bayan bacewar sa.

'Yan sanda sun ce mahaifiyar yaron ta kai rahoton ne bayan ta neme shi ta rasa.

KU KARANTA KUMA: Ina da digiri a fannin hada magunguna da digiri na 2 a fannin tsarin lafiya amma na zabi aikin gyaran jiki domin dogaro da kai - Matashiya

Masu fafutika sun fara kokarin gannin an biya iyalan marigayin diyyar Rand miliyan 3 (kimanin dala 221,000).

Wannan lamarin ya janyo zanga-zanga, inda jama'a suka bukaci a rufe masan domin kiyaye irin wannan abu daga sake faruwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel