Nigerian news All categories All tags
Anyi mare-mare tsakanin kanin gwamna da SSG kan wata kwangila mai gwafi-gwafi

Anyi mare-mare tsakanin kanin gwamna da SSG kan wata kwangila mai gwafi-gwafi

- Majiyar mu tace abin kunyar ya faru ne a ofishin Sakataren Gwamnatin lokacin da kanin gwamnan ya shiga dauko fayel din shi da Mista Agas din ya duba

- Tashin hankalin ya fara ne lokacin da kanin gwamnan ya gane cewa sakataren gwamnatin bai duba fayel din shi ba

- Kowa yasan kanin gwamnan da tunkaho da kuma gadara wanda zai iya harzuka kowa da irin yanayin shi

Anyi mare-mare tsakanin kanin gwamna da SSG kan wata kwangila mai gwafi-gwafi

Anyi mare-mare tsakanin kanin gwamna da SSG kan wata kwangila mai gwafi-gwafi

Mista Tony Okowa, kanin gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta kuma chiyaman din kamashon wasanni, sunyi kaca kaca da sakataren gwamnatin jihar, Mista Festus Ovie Agas, a ranar Alhamis da ta gabata.

Wani ganau ya sanar da majiyar mu cewa " girma ya fadi a yayin da jami'an biyu suka yi musayar yawu har ma da naushi"

Majiyar mu tace abin kunyar ya faru ne a ofishin Sakataren Gwamnatin lokacin da kanin gwamnan ya shiga dauko fayel din shi da Mista Agas din ya duba.

Tashin hankalin ya fara ne lokacin da kanin gwamnan ya gane cewa sakataren gwamnatin bai duba fayel din shi ba.

Wasu jami'an gwamnati da ma'aikatan ofishin sun sanar da majiyar mu cewa abin kunyan ya jawo hankalin mutane da dama saboda masu fadan duk muryoyin su na sama.

DUBA WANNAN: Wahalar rayuwa ta sanya saurayi babbaka kansa a Lagus

"Ina ofishin lokacin da kanin gwamnan ya shigo kuma ya shige ofishin Sakataren Gwamnatin. Jim kadan sai muka fara Jin muryoyin su. Munji sakataren yana cewa 'baka isa ka harzuka ni ba,. Kafin muyi wani yunkuri, mun fara jin karar mari da dambe" inji wani babban jami'i a ofishin.

Kowa yasan kanin gwamnan da tunkaho da kuma gadara wanda zai iya harzuka kowa da irin yanayin shi.

'Akan wanne dalilin zaka mari namiji kuma sakataren gwamna, saboda kana kanin gwamna? Na ga laifin sakataren shima, saboda ya saba ajiye fayil din jami'ai a ofishin shi ba tare da ya taba ba. Wani lokacin sai ka tsayu a kanshi yake dubawa'. Inji wani jami'i.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel