Nigerian news All categories All tags
Hadimin Buhari ya gargadi dan majalisar wakilai kan kiran shugaban Najeriya da ya yi da azzalumi

Hadimin Buhari ya gargadi dan majalisar wakilai kan kiran shugaban Najeriya da ya yi da azzalumi

Mataimakin shugaban kasa na musamman a safukan zumunta, Bashir Ahmad, ya gargadi wani dan majalisar wakilai, Razak Atunwa, kan kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi a matsayin azzalumi.

Atunwa, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kwara ya kira shugaban kasar a matsayin azzalumi a yayinda yake martani ga labarin cewa kotun kolin Najeriya ta wanke shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki sannan kuma ta salami shi akan wasu zarge-zarge uku da ke kansa akan rashin bayyana gaskiyar dukiyoyinsa.

Yayinda yake mayar da martani akan wani rubutu da ya kira Saraki a matsayin shugaban kasa, dan majalisar ya kuma ce duk wani dan Najeriya na da damar zama shugaban kasar Najeriya.

Kalli rubutun a kasa:

Don haka, hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa baza’a taba yarada da kiran Buhari azzalumi ba. Ya yi gargaadin cewa fadar shugaban kasa na iya kai hari amma sun fi son a zauna lafiya.

KU KARANTA KUMA: Bukatu 4 da kungiyar Kiristoci ta mikawa shugaba Buhari

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel