Nigerian news All categories All tags
Yanzu - Yanzu: An sake gurfanar da wani tsohon gwamnan PDP a kotu

Yanzu - Yanzu: An sake gurfanar da wani tsohon gwamnan PDP a kotu

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswan gaban wata babban kotun dake babban birnin tarayya Abuja a yau Juma'a 6 ga watan Yulin shekarar 2018.

An tuhumar Suswan da aikata laifuka guda uku ne wanda suka shafi mallakar bindigogi ba bisa ka'ida ba kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Yanzu - Yanzu: An gurfanar da tsohon gwamnan Benue a kotu bisa laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba

Yanzu - Yanzu: An gurfanar da tsohon gwamnan Benue a kotu bisa laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba

DUBA WANNAN: Muna da rinjaye da zamu iya tsige Buhari a majalisa - rAPC

A baya, hukumar yan sandan farar hula DSS ta kama Suswan a ranar 25 ga watan Fabrairun 2017 bisa tuhumarsa da mallakar wasu filaye da motoccin alfarma da kuma makamai ba bisa ka'ida ba.

Sai dai a wancan lokacin an gaza gurfanar dashi a gaban kotu saboda hukumar DSS a wancan lokacin ta nemi shi ta rasa.

Daga baya, Justice John Tsoho ya dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Mayun 2017.

Bayan wannan tuhume-tuhumen, Suswan kuma yana fuskantar wata tuhumar a gaban wata kotun tarayya dake Abuja.

Ku biyo mu don samun karin bayani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel