Nigerian news All categories All tags
Bukatu 4 da kungiyar Kiristoci ta mikawa shugaba Buhari

Bukatu 4 da kungiyar Kiristoci ta mikawa shugaba Buhari

A ranar Alhamis, 5 ga watan Yuli ne kungiyar kiristocin Najeriya reshen arewacin kasar suka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara.

Sun kaiwa shugaban kasar ziyara ne a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyar ta gabatarwa da shugaba Buhari wasu bukatu da take neman ya cika mata domin magance matsalolin da kasar ke fama da shi na rashin tsaro.

Bukatu 4 da kungiyar Kiristoci ta mikawa shugaba Buhari

Bukatu 4 da kungiyar Kiristoci ta mikawa shugaba Buhari

Ga wasu muhimman bukatu guda hudu da kungiyar ta mika:

1. Kungiyar ta nemi Buhari ya gaggauta yin garambawul a bangaren rundunonin tsaro

2. Sake gyaran dukkanin yankunan da rikicin makiyaya da manoma suka yi sanadiyyar lalacewarsu

3. Samar da cikakken tsaro ga manoma

4. Tilasta makiyaya mallakar filayen kiwo na kansu.

KU KARANTA KUMA: Matasa miliyan 3 za su yi gangami a Kano don nuna hamayya da R-APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Lauretta Onochie tayi amfani da shafin ta na Facebook tayi watsa-watsa da Kungiyar ta CAN. Onochie tace Kungiyar CAN ta Najeriya sun saki layin Ubangiji kuma babu abin da Shugabannin Kiristocin su ke yi sai yaudarar Mabiyan su da nufin tada rikicin addini a cikin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel