Nigerian news All categories All tags
Muna da rinjaye da zamu iya tsige Buhari a majalisa - rAPC

Muna da rinjaye da zamu iya tsige Buhari a majalisa - rAPC

- Buba Galadima ya ce mambobin rAPC suna iya tsige shugaba Buhari cikin sauki saboda su ke da rinjaye a majalisa

- Galadima dai yana cikin na hannun daman Buhari kafin su ware su kafa rAPC

- Galadima da magoya bayansu suna zargin 'yan jam'iyyar APC da kama karya da kuma nuna wariyya

Shugabanin sabuwar APC wanda suka hada kai da 'yan bangaren sabuwar PDP sunce suna da karfin da yawa a majalisar tarayya da za su iya tsige shugaba Muhammadu Buhari idan hakan ta kama.

A ranar Juma'a, Shugaban na rAPC, Injiniya Buba Galadima ya ce "Ina son in fada maka a yadda nake zauna a nan, idan na umurci mambobin mu dake majalisar tarayya su fara shirin tsige shugaban kasa, zasu tabbatar da hakan saboda mu keda rinjaye."

Muna da rinjaye da zamu iya tsige Buhari a majalisa - rAPC

Muna da rinjaye da zamu iya tsige Buhari a majalisa - rAPC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sunyi wa Fulani mummunar ta'asa a jihar Taraba

Galadima ya mayar da martani kan kalaman shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole inda ya yi ikirarin cewa mutanen dake da rAPC basu da wani muhimmanci, yace wanda ke adawa dasu ne basu da nagarta.

Injiniya Galadima wanda yana cikin amintattun jam'iyyar APC kuma tsohon jigo a jam'iyyar CPC, ya yi kira ga 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata su goyi bayan sabuwar jam'iyyar nasu. Jam'iyyar ta rAPC da aka kafa kwananan ne dan nufin ceto 'yan Najeriya daga kangin da suke shiga.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Galadima wanda yana cikin na hannun daman shugaba Buhari a da yana cewa jam'iyyar rAPC ta 'yan Najeriya ce daga kowanne bangare kuma ba ta yarda da nuna son kai da kama-karya ba watau kamar jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel