Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Kotun koli ta wanke Bukola Saraki daga dukkan zargin da gwamnati ke masa

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta wanke Bukola Saraki daga dukkan zargin da gwamnati ke masa

Labarin da ke shigowa yanzun nan na nuna cewa kotum kolin Najeriya ta wanke shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, daga dukkan laifukan da kotun CCT da gwamnatin tarayya ke masa na rashin bayyana kadarorinsa.

Kotun kolin ta tabbatar da shari'ar kotun daukaka kara da Jastis Centus Nweze ya yanke a yau Juma'a, 6 ga watan Yuli, 2018.

Legit.ng ta samu wannan labari ne daga bakin mai magana da yawun shugaban majalisar dattawa, Bamikole Omisore, inda yace: "Kotun koli ta tabbatar da shari'ar kotun daukaka kara kan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, kuma babu wani tuhuma da zai amsa a kotuna CCT."

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta wanke Bukola Saraki daga dukkan zargin da gwamnati ke masa

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta wanke Bukola Saraki daga dukkan zargin da gwamnati ke masa

Zaku tuna cewa a shekarar 2015, gwmantin tarayya ta kai karan Bukola Saraki kotu kan laifin rashin bayyana dukkan kadarorinsa a matsayin ma'aikacin gwamnati wanda kuma ya wajaba akan duk wani mai rike da mukamin gwamnati.

Tun lokacin alkalin kotun CCT, Danladi Umar, ya ke gurfanar da shi amma har ila yau ba'a cimma manufa ba.

Daga baya kuma Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa sun shigar da karan shugaban kotun CCT, Jastis Danladi Umar, a kan cin hanci.

KU KARANTA: Mu na nan a APC babu ruwan mu da R-APC inji wasu Manyan ‘Yan Majalisa

An shigar da karan ne ranan 25 ga wata Fabrairu a babban kotun birnin tarayya Abuja.

A kara na farko, game da cewar takardun da Sahara Reporters, Jastis Danladi Umar, ya bukaci cin hancin N10 million daga hannun wani Mr. Rasheed Owolabi a 2012.

An fara zargin Jastis Umar ne yayinda shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya fara gurfana a kotunsa kan zargin rashin bayyana kadarorinsa a 2015. Daga baya, Umar ya sallami Saraki bayan rahoto ya nuna cewa ya karbi cin hancin $2million daga hannun Saraki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel