Nigerian news All categories All tags
Shugaban Jam’iyyar APC ya gaza cewa komai bayan ya zauna da ‘Yan Majalisa

Shugaban Jam’iyyar APC ya gaza cewa komai bayan ya zauna da ‘Yan Majalisa

Mun samu labari cewa sabon Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshimhole bai iya cewa komai ba bayan ya zauna da ‘Yan Jam’iyyar da ke Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Shugaban Jam’iyyar APC ya gaza cewa komai bayan ya zauna da ‘Yan Majalisa

Shugaban APC Oshimhole yayi gum bayan ya gana da ‘Yan Majalisa

Kamar yadda labari ya zo mana, fusatattun ‘Yan APC da ke Majalisa sun nuna cewa idan ana so a zauna lafiya shi ne a kyale su su koma kujerar su salin-alin a zaben 2019. Hakan ne kurum zai kawo zaman lafiya a cikin Jam’iyyar.

‘Yan Jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Kasar sun koka da yadda ake yi masu rikon wulakanci a Jam’iyyar. Wani ‘Dan Majalisa wanda ya halarci taron da aka yi jiya ya bayyanawa Jaridar Daily Trust wannan ba da dadewa ba.

KU KARANTA:Yan Majalisar APC fiye da 200 sun ki bin su Kwankwaso zuwa R-APC

Shugaban Jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole bai ce komai ba game da bukatar ‘Yan Majalisar na cewa a ba su tikitin tazarce. Sai dai sabon Shugaban na Jam’iyyar yace zai yi bakin kokarin sa wajen ganin an dinke barakar Jam’iyyar.

‘Dan Majalisar yace Gwamnoni sun danne su a Jam’iyya sun kuma daura wadanda su ke so a matsayin shugabanni don haka su ka nemi Shugaban Jam’iyyar ya sasanta banbancin da ke tsakanin Gwamnonin da ‘Yan Majalisar.

Har yanzu dai babu tabbacin cewa an shawo karshen rikicin Jam’iyyar don kuwa kalaman sa ba su nuna wani tabbaci ba. Shugaban Majalisar Wakilan Yakubu Dogara dai yace ayi adalci a Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel