Nigerian news All categories All tags
Zaben Ekiti: Shugaban Jam’iyyar PDP ya caccaki Shugaba Buhari

Zaben Ekiti: Shugaban Jam’iyyar PDP ya caccaki Shugaba Buhari

Mun samu labari cewa jiya Jam’iyyar PDP ta caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kamfen din da tayi na neman Gwamnan Jihar Ekiti da za ayi kwanan nan.

Zaben Ekiti: Shugaban Jam’iyyar PDP ya caccaki Shugaba Buhari

Ba a san Matasan mu da lalaci ba - Inji Shugaban PDP Secondus

A jiya ne Gwamna Ayo Fayose mai shirin barin mulki da kuma Shugabannin PDP da-dama na kasar nan su ka cika Ekiti inda su ka halarci taron da aka ba ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Olusola Kolapo tutar Jam’iyyar mai mulki a Jihar.

Shugaban Jam’iyyar PDP Uche Secondus a wajen taron yayi kaca-kaca da Shugaba Buhari inda ya maida masa martani kan wata magana da yayi a baya game da Matasan kasar. Secondus yace Matasan Najeriya ba Malalata bane.

KU KARANTA: An sa dokar ta-baci a Najeriya saboda cin hanci

Bayan nan dai Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus ya nemi Mutanen Ekiti su zabi Farfesa Olusola Kolapo Eleka na PDP inda yace idan su ka zabi APC, Makiyaya za su yi ta kai masu farmaki su karbe masu kasa.

Manyan Jam’iyyar PDP irin su Atiku Abubakar, da Gwamnoni: Nyesom Wike, Ibrahim Dankwambo, Okezie Ikpeazu, Darius Ishaku, da Emmanuel Udom su na wurin. Haka kuma Ahmed Makarfi da Adolphus Waba‎ra sun samu zuwa

Dazu kun samu labari cewa Gwamna Ayodele Peter Fayose na shirin mikawa Shugaban kasa Buhari kokon baran sa game da zaben na Jihar Ekiti domin ganin an yi adalci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel