Nigerian news All categories All tags
Sanatan Jihar Kaduna na kokarin ganin an kafa sabuwar Jami’a a Zaria

Sanatan Jihar Kaduna na kokarin ganin an kafa sabuwar Jami’a a Zaria

Mun samu labari a makon nan cewa Majalisar Dattawan Najeriya na nema a kafa wata Jami’a ta musamman ta ilmi a Jihar Kaduna da ke Arewacin kasar. Yanzu har maganar tayi nisa a Majalisa.

A zaman da Majalisar Dattawan Najeriya tayi a makon nan, ta tabo maganar gina Jami’a ta Ilmi a Garin Zaria da ke cikin Jihar Kaduna. An tattauna wannan batun a Majalisar kuma nan gaba za a ji matsayar da Majalisar ta dauka.

Sanatan Jihar Kaduna na kokarin ganin an kafa sabuwar Jami’a a Zaria

Shehu Sani yace maganar kirkiro Jami'a a Zaria tayi nisa a Majalisa

Sanata Shehu Sani wanda shi yake wakiltar Yankin Kaduna ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar APC ya fadawa Duniya wannan jiya. Sanatan ya bayyana wannan ne a shafukan sa na sada zumunta na zamani na Tuwita da kuma Facebook.

KU KARANTA: Jami'a sai su wane da wane yanzu a Najeriya

‘Dan Majalisar yake cewa su na aiki kan wani kudiri na kirkiro wasu Jami’o’i wanda har an yi nisa. Daga cikin Jami'o'in da ake shirin kafawa akwai Jami’ar ilmi a Zaria. Haka kuma ana nema a maida Makarantar kwarewa a aiki ta Kaduna Jami’a.

A mako mai zuwa ne kuma ‘Dan Majalisar yace za su tattauna game da kokarin ganin an maida Kwalejin fasaha da kwarewan aiki ta Yaba ta zama babbar Jami’a. Haka dai kuma an sa rai a maida Takwarar ta da ke Kaduna ta zama Jami’ar.

Idan ba ku manta ba dai a shekarar 2014 tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya maida wasu kwalejin ilmi na kasar zuwa Jami’a. Daga ciki akwai FCE Zaria da ta Owerri da wata da ke Jihar Ondo da kuma kwalejin koyon ilmi na Alvan Ikoku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel