Nigerian news All categories All tags
Mu na nan a APC babu ruwan mu da R-APC inji wasu Manyan ‘Yan Majalisa

Mu na nan a APC babu ruwan mu da R-APC inji wasu Manyan ‘Yan Majalisa

- Wasu manyan Jam’iyyar sun ki shiga cikin sabuwar R-APC

- Daga ciki akwai Sanatoci fiye da 50 da wasu ‘Yan Majalisu

- Wasu daga cikin ‘Yan APC dai tuni su ka balle zuwa R-APC

Mun kuma samu wani sabon labari cewa ‘Yan bangaren R-APC wadanda su ka bangare daga Jam’iyyar APC mai mulki za su gamu da cikas bayan ‘Yan Majalisa da-dama sun yi zaman su a APC.

Mu na nan a APC babu ruwan mu da R-APC inji wasu Manyan ‘Yan Majalisa

Wasu ‘Yan Majalisa ba zu bi su Kwankwaso zuwa R-APC ba

Da alama dai kokarin da ake yi na kawo rabuwar kai a Jam’iyyar APC mai mulki ba zai kai ko ina ba don kuwa Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu manya a Jam’iyyar APC a kasar sun nuna cewa babu inda za su tafi.

Daga cikin wadanda su ka nuna ba za su bi tafiyar R-APC na sababbin ‘Yan tawaren ba akwai manyan Sanatoci irin su Abdullahi Adamu; Aliyu Wammako; Danjuma Goje; Adamu Aliero; da kuma Sanata Kabiru Gaya.

A takaice dai wasu tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar PDP da ke Majalisar Kasar wadanda ake kira nPDP da dama sun yi watsi da tayin R-APC. Sanatoci akalla 52 da ‘Yan Majalisar Wakilai 184 sun ce ba za su bar Jam’iyyar APC ba.

KU KARANTA: Ana daf da karbe rinjayen Majalisa a hannun Jam’iyyar APC

Kamar yadda labarin ya zo mana, bayan nan kuma wasu Gwamnonin Jam’iyyar irin na Kogi Yahaya Bello da Jibrilla Bindow na Jihar Adamawa da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje sun nuna babu su babu wata R-APC.

A Jihar Kano Sanatocin Jihar 2 da kuma ‘Yan Majalisa 14 cikin 24 na Jihar ba su tare da Kwankwaso a yanzu. Ba mamaki dai irin su Bukola Saraki, Monsurat Sunmonu; Isa Misau; Dino Melaye su bar Jam’iyyar APC.

Sauran ‘Yan R-APC a Majalisar sun hada da irin Soji Akanbi; Shehu Sani: Suleiman Hunkuyi; Mohammed Sha’aba Lafiagi; Rafiu Ibrahim; Kabiru Marafa; Aliyu Sabi Abdullahi da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel