Nigerian news All categories All tags
Fayose na neman ya gana da Shugaba Buhari saboda Zaben Jihar Ekiti

Fayose na neman ya gana da Shugaba Buhari saboda Zaben Jihar Ekiti

Mun samu labari cewa Mai girma Gwamna Ayodele Peter Fayose na shirin mikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kokon baran sa game da zaben sabon Gwamnati da za ayi a Jihar sa ta Ekiti nan da 'yan kwanaki kadan.

Fayose na neman ya gana da Shugaba Buhari saboda Zaben Jihar Ekiti

Fayose na kokarin ganin Mataimakin sa yayi nasara a zaben Jihar Ekiti

Gwamna Ayo Fayose yayi hira a gidan Talabijin na EKTV yace zai yi kokarin zuwa ya samu Shugaban kasa Buhari ya roke sa cewa ka da a zuba Sojoji na babu gaira babu dalili a zaben da za ayi kwanan nan a Jihar Ekiti.

KU KARANTA: Buhari ya sa ha hannun kan wata ssabuwar doka a Najeriya

Ayo Fayose wanda rikakken ‘Dan adawan Shugaban kasar ne yace wannan karo zai yi kokarin ya nemi alfarma domin ganin ba ayi amfani da Sojoji wajen murde zaben Jihar ba kamar yadda aka yi a zaben da aka yi a baya.

Ana zargi dai PDP tayi murdiya a zaben da Ayodele Fayose yayi nasara a 2014 inda ya buge Kayode Fayemi na Jam’iyyar APC. A lokacin Jonathan an yi amfani da Sojojin kasar wajen murde zaben na Gwamnan Ekiti.

Gwamnan na Ekiti dai ya sha alwashin ganin Jam’iyyar sa ta PDP ta lashe zaben da za ayi. Kwanaki kun ji yadda Shugaba Buhari yayi Allah-wadai da zaben na 2014 yana mai nuna takaicin abin da ya faru a lokacin zaben.

.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa K

o a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel