Nigerian news All categories All tags
R-APC: Jam’iyyar PDP ta kerewa APC yawan ‘Yan Majalisa

R-APC: Jam’iyyar PDP ta kerewa APC yawan ‘Yan Majalisa

Bisa dukkan alamu dai da zarar an yi sake Jam’iyyar APC za ta rasa rinjayen da ta ke da shi a Majalisar Dattawan Najeriya saboda rikicin da ya barke har ta kai wasu su ke shirin tserewa daga Jam’iyyar su sauya sheka.

R-APC: Jam’iyyar PDP ta kerewa APC yawan ‘Yan Majalisa

Maganar karbe rinjaye daga APC na nema ta tabbata

Tsofaffin ‘Yan nPDP da ke cikin Jam’iyyar APC mai mulki sun bangare inda su ka kafa wata sabuwar Kungiya mai suna R-APC wanda tsohon Sakataren Jam’iyyar CPC Injiniya Buba Galadima yake shugabanta.

KU KARANTA: Za a bar APC saboda rashin adalcin Jam'iyyar - Shehu Sani

Yanzu dai ana kishin-kishin din cewa ‘Yan R-APC a Majalisar Dattawa su na nema su fi ‘Yan Jam’iyyar APC na ainihi yawa. Kusan Sanatocin da ke bayan R-APC sun kai 26 yayin da 24 ne ke tare da ainihin Jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PDP dai tana da Sanatoci 39 a Majalisar Dattawan Kasar a yanzu. Daga cikin manyan Sanatocin da ke tare da R-APC akwai Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso da wasu ‘Yan Majalisar Arewa da-dama.

Bayan nan kuma akwai Sanatoci 2 da ke karkashin Jam’iyyar adawa ta APGA a Majalisar Dattawan kasar. Dama kun ji cewa Sanatan APC Shehu Sani ya bayyana cewa wasu za su tattara su tsere daga Jam’iyyar APC kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel