Nigerian news All categories All tags
Jama’a da dama za su fice daga Jam’iyyar APC – Shehu Sani

Jama’a da dama za su fice daga Jam’iyyar APC – Shehu Sani

Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya Shehu Sani ya bayyana cewa shakka babu wasu za su tattara su tsere daga Jam’iyyar APC mai mulki.

Jama’a da dama za su fice daga Jam’iyyar APC – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yace za a tsere daga Jam'iyyar APC

‘Dan Majalisar Kasar yayi wannan jawabi ta shafin sa na Tuwita cikin azanci kamar yadda ya saba. Sanatan na APC yake cewa zaluncin Jam’iyyar ta sa dole wasu za bar ta. Kwanaki dama Sanatan yayi irin wannan magana.

KU KARANTA: Jerin 'Yan siyasan da su ka bar APC a Kaduna

Fitaccen Sanatan da ke wakiltar Kaduna a a Majalisa yake cewa akwai ‘dan karen zalunci da rashin adalci a Jam’iyyar don haka ne ire-iren sa wadanda aka taso gaba za su tsere domin su samu mafita a harkar siyasar kasar.

Sanatan yayi wannan magana ne ba da dadewa ba a shafukan sa na yada labarai inda ya tabbatar da maganar da yayi kwanaki na cewa yace ta zama dole su bar Jam’iyyar domin babu wani dalilin cigaban su na zama saboda zalunci.

Yanzu haka dai wasu da-dama sun balle daga Jam’iyyar APC inda su ka kafa wata kungiya da ta bangare mai suna R-APC karkashin shugabancin Buba Galadima. Bayan nan dai Sanatan yayi ta’aziyyar rashin Malam Adamu Ciroma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel