Nigerian news All categories All tags
Rikedewar nPDP zuwa rAPC: APC ta nesanta Buba Galadima da jam'iyyarta, ta ce ba ta da wani tsagi

Rikedewar nPDP zuwa rAPC: APC ta nesanta Buba Galadima da jam'iyyarta, ta ce ba ta da wani tsagi

A yau, alhamis, APC mai mulki tayi magana a kan rahoton wani tsagin jam’iyyar da ‘yan nPDP suka kirkira (rAPC) kuma suka nada Buba Galadima a matsayin shugabanta.

A wani jawabi da kakakin APC, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewar shugabannin tsagin rAPC ba halastattun ‘yan APC ba ne.

A ranar laraba, 4 ga watan Yuli, 2018, wasu mutane sun bayar da sanarwar kafa wata kungiya da suka kira ‘Reformed All Progressive Congress (rAPC). Abinda wadannan mutane suka yin a nuna tamkar jam’iyyar APC na da wani tsagi bayan kuma hakan ba gaskiya bane.

Rikedewar nPDP zuwa rAPC: APC ta nesanta Buba Galadima da jam'iyyarta, ta ce ba ta da wani tsagi

Buba Galadima da 'yan nPDP

“APC na mai sanar da jama’a cewar babu wani tsagi a cikinta, a saboda haka bat a tare da wadannan mutane dake shirin bata sunan jam’iyyarmu.

Jawabin ya kara da cewar, “mutanen na yin hakan ne bayan yunkurinsu na kawo rudani yayin zabukan shugabannin jam’iyyar APC bai cika ba. Mutanen dake ikirarin shugabancin wannan kungiya ba ma ‘yan jam’iyyar APC bane.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Buhari ya yi doka a kan kadarorin gwamnati da aka kwato

“zamu ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da hadin kai a cikin jam’iyyar mu, kuma zamu kare jam’iyyar mu daga masu kokarin kassara ta.

“’ Mambobin jam’iyyarmu dake da korafi, muna masu tabbatar masu da cewar sabon shugabancin jam’iyyar APC zai yi masu adalci.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel