Nigerian news All categories All tags
Shugaban kasan Najeriya da na Faransa sun shiga wata yarjejeniya

Shugaban kasan Najeriya da na Faransa sun shiga wata yarjejeniya

- Shugaban Kasar Faransa ya kawo ziyara a Najeriya kwanan nan

- Faransa za ta kashe Dala Miliyan 475 a wasu Garuruwan kasar

- Kasar Faransar za ta kashe kudin ne a Ogun da Legas da Kano

Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu kan wasu yarjejeniya na makudan miliyoyi na Dalolin kudi da Kasar Faransa kan wasu ayyuka da za ayi a Najeriya.

Shugaban kasan Najeriya da na Faransa sun shiga wata yarjejeniya

Buhari tare da Shugaban kasan Faransa a Abuja kwanaki

A jiyan nan ne Fadar Shugaban kasa ta bayyana Najeriya ta shiga wata yarjejeniya ta Dala Miliyan 475 da kasar Faransa. Kasar ta Faransa za ta ginawa Najeriya abubuwan more rayuwa a wasu manyan Garuruwa na kasar.

KU KARANTA: Abin da ya sa na shiga PDP - Ahmed Buhari

Wani Hadimin Shugaban kasa kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmaad yayi bayani a shafin sa na Tuwita cewa Faransa za ta gina abubuwa na jin dadin rayuwa da raya birane a cikin Garin Legas da ke kudancin Najeriya.

Faransa ta kuma yi alkawarin aikin ruwa a Garin Kano. Har wa yau akwai wasu ayyukan da Kasar ta Turai za tayi a Jihar Ogun. Kasar ta Faransa dai za ta kashe sama da Dala Miliyan 400 a Najeriya kamar yadda mu ka ji.

Kwanaki da Shugaban Faransa ya kawo ziyara kun ji labari cewa Shugaban kasar watau Emmanuel Macron yayi zaman Najeriya a lokacin da yake koyon aiki a ofishin Jakadancin Kasar Faransa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel